Duba kasar Afrika tilo da ba a yi wa mulkin mallaka ba mai wata 13 marmakin 12 a shekara

'

Yan Ethiopia na fara sabuwar shekararsu da cin abinci tare da iyalai daban-daban a lokaci guda, duk da matsananciyar rayuwar da ake fama da ita da tashin farashin kaya da yunwa da ta mamaye yankin arewaci.

Karanta karin bayanai game da tsarin kalandarsu ta musamman da kuma al'adunsu.

1) Wata 13 ne ke yin shekara daya

Ba wannan ba ma - kalandar Ethiopia tana bayan ta kasashen yamma da shekara bakwai da wata takwas, inda ranar Asabar ta zama farkon shekarar 2014.

Wannan ko ya biyo bayan kidayar shekarar haihuwar Annabi Isa da suke yi daban da na wadannan kasashe.

Lokacin da Cocin Katolika ta sauya kirgenta a shekarar 500 AD (bayan wafatin Annabi Isa), amma a lokacin Cocin Latolika ta Ethiopia ba ta sauya tata kalandar ba.

Don haka shekarar ta fado a ranar 11 ga watan Satumba a kalandar kasashen Yamma, wannan daidai da lokacin bazara kenan.

'Yan kabilar Oromo na bikin Irreecha a Ethiopia a 2017.

Bayanan hoto, Yayin bikin Irreecha na 'yan kabilar Oromo, akan yankar sabbin ciyawa a rika sanya wa a ruwa a matsayin godiya ga Allah da ya kawo yanayin bazara.

Yaran Ethiopia ba irin na ko ina ba ne, domin kuwa su da sun fara girma ake koya musu wake da za su rika tuna kwana nawa ne a kowanne wata.

Abin ba shi da wuya sosai a Ehiopia: wata 12 na farkon shekera duka suna da kwanaki 30, sai na 13 da ke yin kwana biyar ko shida, ya danganta da yanayi a shekarar.

Yadda ake duba lokaci shi ma na da banbanci - lokacin ana raba shi biyu ne, awa 12 da ke fara wa daga karfe 6:00 wanda yake a matsayin maraice da kuma cikin dare, zuwa shidan safe.

2) Ita ce kasar Afrika tilo da ba a yi wa mulkin mallaka ba

Italiya ta so yi wa Ethiopia ko in ce Abyssinia kamar yadda ake kiranta a 1895 mulkin mallaka, lokacin da kasashen Turai ke ta hankoran kasafta kasashen nahiyar a tsakaninsu - sai dai mutanen Italiyan sun kare da jin kunyar gaza shiga kasar.

Italiya ta yi wa makociyar kasar Eritrea mulkin mallaka lokacin da wani kamfanin Italiyan ya sayi tashar jirgin ruwa da ke Assab.

Kuma an shiga rudani ne bayan mutuwar sarkin Habasha Yohannes IV a 1889 wanda ya ba su damar amfani da wani tudu da ke kusa da teku.

Shekaru kadan Italiya ta yi yunkurin kara kutsawa Ethiopia, amma ta kwashi kashinta a hannu a yakin da aka kira da yakin Adwa.

Cikin 'yan sa'o'i aka murkushe wasu manyan kwamandojin Italiya a ranar 1 ga watan Maris din 1896 lokacin da mayakan sarki Menelik II suka afka musu.

An matsa wa Italiya ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da za ta tabbatar da 'yancin kan Ethiopia - duk da dai bayan shekaru kusan goma Shugaba Benito Mussolini ya yi watsi da ita, ya kuma mamaye kasar na kusan shekara biyar.

Daya daga cikin wadanda suka gajin Menelik, Sarki Haile Selassie ya ci gajiyar nasarar da ya samu a kan Italiya ta yadda ya kirkiri kungiyar hadin kan kasashen Afrika wadda a yanzu ake kiranta AU da ke da hedikwatarta a Addis Ababa babban birnin Ethiopia.

Lokacin kaddamar da kungiyar a 1963 Selassie ya ce "Yancin da muka samu ba shi da wata ma'ana har sai sauran kasashen Afrika sun samu 'yanci" lokacin da kuma mafi yawan kasashen nahiyar ba su samu 'yancin kai ba.

3) Basarake Haile Selassie Wanda masu bin addinin Rastafarian ke bauta masa

Wannan ya faro ne lokacin da wani jagoran fafutukar 'yancin bakar fata Marcus Garvey, ya yi bayani a 1920, wanda shi ne jagoran wata tafiya da aka yi wa take da 'Mayar da bakaken fata Afrika', inda ya ce "ku yi duba zuwa Afrika lokacin da za a nada wa wani sarki sarauta ranar 'yanci na kusa."

Shekara 10 baya, lokacin da wani matashin mai shekara 38 Ras Tafari aka nada shi a matsayin Haile Selassie I, da yawa a Jamaica na kallan wannan tafiya kamar ta annabta. A nan aka fara tafiyar Rastafari.

A mural depicting Ethiopian Emperor Haile Selassie I, Jamaican Reggae legend Bob Marley and his sons at grounds of the Bob Marley Museum in Kingston, Jamaica, on May 2019

Mawakin nan Bob Marley na daya daga cikin mutanen suka rika yada sakon Rasta - a wakokinsa.

Wannan fefen da Bob Marley ya yi, jaridar Time Magazine ta ayyana shi a matsayin fefen da ya fi ko wanne a a karni na 20. wanda ya nuna bukatar Rasta ta mayar da mutanen Afrika gida. Wadanda aka tilasta wa zuwa Turai lokacin mulkin mallaka.

Asalin hoton,

Dubban mabiya addini Rastafara ne suka fito suka gaida Sarkin na ethiopia lokacin da ya je ziyara Jamaica a 1966.

A yau masu bin addinin Rastafara kalilan ne ke rayuwa a wani yankin Ethiopia da ake kira Shashamene, mai nisan kilomita 225 daga kudancin Addis Ababa, a wani lardi da Sarki Selassie ya bayar domin bakaken fata da ke shirin dawowa daga kasashen yamma wanda ya goyi baya.

Sarki Selassie wanda mabiyin addinin Kirista ne ba mabiyin addinin Rasta ba ne, ya kuma jaddada cewa shi ma zai mutu, amma har yau masu bin addinin Rasta na kallonsa a matsayin zakin Judah.

Wannan wata hujja ce akan zargin cewa abin bauta ne shi, wanda mabiya Rastafara da kuma 'yan Ethiopia suka yi amannar cewa an yi bayaninsa a Injila Sarki Solomon.

4) Gidan akwatun alƙawari

A wajen da yawa daga cikin Ethiopia, akwai gidan wani akwati da suke da yakinin sakon da za su yi amfani da shi yana ciki.

Cocin Katolika da ke Ethiopia ta ce wannan akwati na karkashin kulawa ta musamman a cocin Lady Mary inda ba a barin kowa ya shiga ya ganta.

Yadda ƴan ci-rani ke kwarara Saudiyya a hanya mai cike da hatsari

A al'adance cocin na da kayayyakin tarihin Sarauniya Sheba, wadda masu tarihi ke musanta samuwarta, amma dai ba 'yan Ethiopia ba ne da wannan aiki.

Sun yi amannar cewa ta yi tafiya daga Aksum zuwa Birnin Ƙudus domin ta ziyarci Sarki Solomon da kuma kara sanin baiyar da yake da ita a shekara ta 950 kafin zuwan Annabi Isa.

Labarin tafiyarta da haɗuwarsu da Solomon yana cikin Littafin Kebra Nagast - Littafin adabin Ethiopia da aka rubuta da yaren Ge'ez a karni na 14.

An bayyana yadda Sarki Makeda da Sarauniya Sheba suka haifi ɗa, Menelik - da kuma yadda bayan shekaru ya tafi Birnin Ƙudus domin haɗuwa da mahaifinsa.

Solomon ya so ya zauna tare da shi ya ci gaba da mulki bayan mutuwarsa, amma daga baya ya yarje masa ya koma gida, ya kuma tattara masa labaran Isra'ilawa - wanda aka sace na ainihin aka sauya shi da na bogi.

5) Gidan Musulman farko da ke wajen yankin Larabawa

"Idan kuka je Absyssinia, za ku tarar da wani sarki da baya goyon bayan rashin gaskiya," Annabi Muhammad SAW ya gaya wa sahabbansa lokacin da aka matsa musu Makka za su yi hijira a karni na 7 inda yanzu ake kira Saudiyya.

Inda Najjashi ya zauna nan ake kira Tigray a yau, nan ne wadannan 'yan gudun hijirar suka zauna suka gina masallacin da ake ganin ya fi ko wanne daɗewa a nahiyar Afrika. A bara ne aka ruguza wannan masallaci lokacin da ake rikicin yankin Tigray.

Wannan ya faru ne lokacin da Annabi ya fara kiraye-kirayen zuwa ga Musulunci, wanda shugabannin da ba Musulmai ba na lokacin ke masa kallon wata barazana.

Bayan sun yi abin da ya ce, wasu daga cikin tsirarin Musulmai sun isa masarautar Aksum, wadda a baya ta hada da Ethiopia ta yau da Eritrea, inda aka karbe su hannu bibiyu karkashin wani sarkin Kirista na masarautar Amhara - wanda ake kira Nejjashi da Larabci.

Inda Najjashi ya zauna nan ake kira Tigray a yau, nan ne wadannan 'yan gudun hijirar suka zauna suka gina masallacin da ake ganin ya fi ko wanne daɗewa a nahiyar Afrika. A bara ne aka ruguza wannan masallaci lokacin da ake rikicin yankin Tigray.

Musulmai da yawa sun yi amannar an binne sahabbai da yawa a garin Nagesh.

A tarihin Musulunci wannan tafiyar da sahabban suka yi zuwa Masarautar Aksum a matsayin hijirar farko a addinin.

A yau adadin Musulman da ke zaune a Ethiopia sun kai kashi 34 cikin 100 ko kuma sama da Musulmai miliyan 115 da ke zaune a kasar.

BBC Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN