Type Here to Get Search Results !

Irin Macizan da suka fi hadari a Duniya da riga-kafin cutarwarsu – Dakta Umar


Wani masanin macizai da ya yi
kwakwasai da dama a kan rayuwarsu, Dakta Umar Garba, da ke Samarun Zariya, a Jihar Kaduna, ya yi bayani dalla-dalla na matakai da ya kamata a dauka don ceto wanda maciji ya sara, ta yadda za a ceto rayuwarsa.

Dakta Garba Umar wanda aka fi sani da Ubale Mai Maciji, ya yi wadannan bayanan ne a tattaunawarsa da wakilanmu lokacin da ya zo Shirin rediyo da talabijin mai taken Barka Da Hantsi Nijeriya na Kamfanin LEADERSHIP da ake yadawa kai-tsaye ta kafar YouTube da Facebook.

Ya fara da bayyana na’u’o’in macizai a doron kasa, “Gaskiya kowace kasa da irin nata nau’in macizan, amma dai macizan da suka fi hadari, kasashe uku a duniya su ne suke nau’in macizan da suka fi hadari, kamar Nijeriya, Afirka ta Kudu da Australia, su suka da macizai masu hadarin gaske, irin su Kasa, Kubuwa, Gamsheka, wadannan macizai sun fi ko wane maciji hadari a duniya” in ji shi.

Wadannan macizai idan suka yi cizo in ba a dauki mataki na gaggawa ba sai ka ga an rasa rai, kuma duk da cewa mutane suna tsoron maciji, ya dace a dage a samu ilimi a kai, saboda akwai karancin makaranta da masu bincike a kai, akwai masu binciken amma ba irin yadda muka yi ba. Saboda kamar ni yanzu idan ka ce min maciji kaza, to sai na kamo shi na ga irin halayyarsa, na ga rayuwarsa da abin da yake so na ga abin da ba ya so, sannan mu ga yaya dafinsa yake illa a jiki, idan kuma dafin ya shiga jikin mutum ya za a samu a duba shi, to ka ga duk irin wadannan suna da muhimmanci.

Daktan, ya bayyana yadda za a ba wa mutumin da maciji ya sara taimakon farko kafin a kai shi asibiti ko wajen likita, inda ya ce; gaskiya akwai abin da ake yi a wanda ko a asibiti bai kamata ba. Idan maciji ya yi cizo a kan daure kafa wanda bai dace a daure ba, ko harbin kunama bai dace a daure ba. Domin idan gudu ake yi kada dafin ya bi jini, ai idan ka je asibiti sai ka tsaya tsawon awanni uku na bincike kafin a baka wani magani.

Idan ka daure wajen zai kumbura, kuma da ya kumbura zai iya jawo shanyewar jiki ko wani raunin, to bai dace a daure ba. Idan mutum maciji ya cije shi idan ya tabbatar har macijin ne, to sai ya tashi daga inda macijin ya cije shi don kada ya kara masa, kada ya yi tafiya da kafarsa kuma kada ya zauna a rana, saboda zafin rana yana kara sa dafin ya yi tasiri a jikin mutum, to sai ya mutum ya nemi inuwa ya zauna, idan a gari ne a nemo ruwan kankara a kofi a dinga bashi kada-kadan yana sha, saboda dafin maciji ba ya tasiri a wurin da sanyi yake, to yana sha zai mayar da dafin nan inda yake ba zai tasiri ba, daga nan sai a samu wanda zai dauke shi zuwa asibitin.

Sannan a asibitin ma akwai abin da ake yi da bai kamata ba, shi ne ba wa wanda maciji ya sara abinci, ba a so a ba wa wanda maciji ya sara abinci domin zai rika kartarsa ne a ciki, kuma da zarar ya fara kartarsa a ciki jini zai fara bulbula. Don haka duk abin da za a ba wa wanda maciji ya ciza ya zama mai ruwa ne kuma da sanyi sosai, sannan kada a bar shi wurin da yake da zafi, dole a sanya fanka ta rika busa musa lokacin da ake yi wa mutum magani, rashin sanin haka ne ke kawo yawan mutuwa.

Haka zalika, ya bayyana wasu hanyoyi da mutane don za su bi don kare kansu daga farmakin maciji inda ya ce, “To a yanzu koken da muke samu game da maciji, sai ka ji maciji ya ciji mutum a cikin gida, ko kuma macijin ya zo ya zauna a bandaki, to irin wadannan, su mutanen ne su ke jawo macizan cikin gidajensu. In dai kana share gidanka ya zama babu wani wuri da maciji zai buya to ba za su zauna ba.”

Ya kara da cewa, bugu da kari mafi yawan abin da yake kawo maciji cikin gida shi ne, a ci kwai a bar bawon kwan a cikin gida, ko kuma a rika kiwon kaji suna yin kwai a gida, ka ga sun samu gurbi kenan a cikin gida. Saboda maciji na jin kamshin bawon kwai daga nisan tafiyar Kilomita 15, domin babu wata halitta da ta kai shi ji, sannan babu halittar da kai shi dadewa a duniya.


“Ni dai Musulmi ne na yi bincike, amma duk binciken da zan yi ba na bari abin ya wuce addinina, saboda za ka ji mutane na karya suna cewa akwai maciji aljani, a’a, duk wata Kimiyya da za ka gani ko menene, babu abin da Alku’ani ya bari. Kuma ka san mutanenmu akwai yaudara musamman masu hulda da macizai akwai karairayi da yawa, wanda bai dace ba. Shin ka taba ganin mai irin wannan sana’ar ya yi kudi, ba’a yin kudi da sana’ar, su da masu sayar da magani ba sa yin kudi, kuma ko da mutum ya yi ma za su kare, domin ka yi ta rantsuwa a kan karya to duk abin da za ka samu ba zai albarka ba,” in ji shi.

Haka zalika ya bayyan wani lokaci da ya ce a rayuwarsa ya taba wani hatsabibin maciji, macijin da ya ciji mahaifiyar Shugaba Obasanjo a lokacin da yana mulki, “A gaskiya shi ne hadarin maciji da na fara gani, domin ni ban taba tunkarar maciji na tsorata da shi ba, amma wannan sai da ya sa gabana ya fadi duk da wani abu aka yi a kan macijin, babu kasar da ba’a kaita ba, an kaita Jamus, an kaita Australia duk sun ce ba za su iya ba.

Da suka Ingila to malamina yana Ingila, shi ne mataimakin shugaban Jami’ar Odford ana kiransa Dabid Warral, ya tsaya iya bincikensa saboda a duniya babu wanda ya kai shi sanin maciji amma shi wannan ya fi karfinsa, amma akwai wani yaro a Nijeriya, sai ya ba da lambata.

Karfe biyun dare ina bacci a gidana na Nyanya, El-rufa’i ya kirawo ni ya ce Shugaban kasa yana nemanka kuma kira na gaggawa, na ce me ya faru ya ce dai ana son ganinka, kafin ma na gama shiryawa SSS suna kofar gida suna jirana,” in ji shi.

Ya cigaba da cewa, yana zuwa ya ganta a kwance, ya duba ya ga duk abin da yake faruwa, aka basu mota suka tafi. “A gaskiya ban taba haduwa da hadarin maciji irin wannan ba, ka ga dai na taba kama wani hatsabibin macijin da ina kama shi kayan jikina suka kama da wuta, amma duk ban dauke shi a kan wani abu ba, amma shi wannan na mahaifiyar Obasanjo din na kama shi mun saka shi a mota muna tafiya, duk wadanda suke cikin motar suka fado ba mu sani ba.

Idan an sanya shi a kwati an kulle sai ka zo ka same shi a saman akwatin kuma ga ta a kulle ba mu bude ba, to shi kadai ne kawai ya bani tsoro. Amma za ka ji mutane na cewa aljanu a’a duk abin da kake yi ka rika waiwayon addinika to ba za ka shiga duhu ba,” a cewarsa.

Daktan ya cigaba da cewa duk macijin da ya kai shekara 250 zai iya canjawa, amma ba aljani ba ne. Ko mutum ne ya cika shekara 250 sai ka ga yana rikida, to maciji na shekara 500 a duniya, da maciji da Kunkuru da Kada suna shekara 500 a duniya, shi ne mutane ke cewa aljanu ne, kuma duk lokacin da ka ga aljani to sai ka rasa hankalinka, don ba za ka iya bayar da bayani ba.

Daga karshe ya bayyana alakarsa iyalansa da maciji, inda ya ce; “To wanda ya shigo gidanmu ya san akwai maciji, duk maganin da ka ga na samar daga ni ya fito, shi ya sa ko shiri nake zan fito kai tsaye na gaya maka na san babu wata tambaya da za ta gagare ni, ko ta halin yaya ba za a kure ni a kan maciji.

Rahotun Leadership Hausa

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies