Gwamna Babagana Umara Zulun ba jihar Borno a ranar Laraba ya zargi daukan jami'an tsaro da hukumomin tsaron Najeriya ke yi aiki da saka siyasa a lamarin, abinda ke saka fannin tsaron kasar nan cikin mawuyacin hali.
Zulum na yin jawabi ne mai take 'Ungoverned Space and Insecurity in the Sahelian Region: Implications for Nigeria Domestic Peace and Security' a NIPSS da ke Kuru, jihar Filato, Daily Trust ta wallafa.
Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, ya ce:
"Babbar matsala da ake samu wurin daukan aiki ne. Wadanda ake dauka aiki a rundunar sojin kasa, 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro duk masu neman aiki ne. Da yawa daga cikinsu sun je wurin ne saboda ba su da aikin yi.
"Wadanda aka dauka a shekaru 20 da suka gabata sun fi aiki mai kyau amma wadannan masu neman abun yin aiki kawai suke so a basu. Don haka babu mayar da kai tare da sadaukarwa a ayyukansu.
"A yanzu, gwamnoni, ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati su ke da guraben aikin. Babu mai yi musu jarabawa ko sun dace da aikin ko akasin hakan. Daukar aikin soja, 'yan sanda da sauransu duk an siyasantar."
Gwamnan ya kara da cewa:
"Har sai mun yi a kan gyara komai, babu abinda zai sauya a kasar nan.
"Idan muna son cigaba, dole ne mu tantance abinda ya fi kyau. Idan ba haka ba, za mu cigaba da daukan sakarkaru aiki. Dole ne mu dauka wadanda za su iya abinda mu ke so saboda muna da masu kwazo da yawa a Najeriya."
Legit