Gwamna Ortom Ɗan Bindiga Ne, 'Yan Bangan Mu Za Su Kama Shi, Miyetti Allah


Kungiyar fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta kira gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai da dan ta’adda, kuma ta lashi takobin kama shi matsawar EFCC ba ta damke shi ba.

Kungiyar ta yi wannan furucin ne bayan gwamnonin kudu sun hana kiwon shanu a fili, dokar da suke dab da kafawa

Miyetti Allah ta zargi gwamna Ortom kwarai inda ta ce dan ta’adda ne shi. Ta kuma bayyana wannan zargin ne ta sakataren ta na kasa, Saleh Alhassan, ya yin tattauna wa da gidan jaridar Leadership.

$ads={2}Miyetti Allah ta lashi takobin sanya ‘yan sintirin ta su kama gwamnan bayan ya sauka daga kujerarsa.

Sannan Alhassan ya zargi gwamnan da fada da kungiyar fulanin.

Dakatar da kiwo a fili zalunci ne kuma ba za mu taba amincewa da hakan ba,” a cewarsa.

Idan kana neman gawurtaccen dan ta’adda, ka nemi gwamna Ortom na jihar Binuwai. Don shi ne asalin dan ta’adda.

$ads={2}Alhassan ya zargi gwamnan da satar dukiyar jihar Binuwai. Ya kuma bayyana cewa matsawar EFCC ba ta kama shi ba, ‘yan Sintirin Miyetti Allah za su kama shi.

Kamar yadda yace,:

Jiran shi muke yi ya sauka daga mulki, matsawar EFCC ba ta damke shi ba, ‘yan sintirinmu za su damke shi.

Legit

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari