Fitaccen Malamin, Zakir Naik yana nema wa ɗan shi matar aure


Fitaccen malamin addinin musulunci, Zakir Naik ya yi wata wallafa a shafin sa na Facebook inda ya ke nema wa dan sa Fariq Zakir Naik matar aure.

A cewar sa, ya na nema wa dan sa Fariq mata musulma mai tarbiyya mai kyau yadda za su kasance fitilu masu haska wa juna rayuwa.

A wallafar wacce yayi ta shafin sa na Facebook, ya ce mahaifi ko waliyyin matar ya yi masa magana da kuma bayanan da ake bukata.

Kamar yadda ya wallafa:

"Ina nema wa da na Fariq matar aure, musulma ta kwarai mai dabi’u masu kyau yadda da na da matar sa za su kasance haske ga juna.

"Idan kai mahaifi ko kuma dan uwa wanda ya amince da wannan ne, ya yi gaggawar kawo bayanai."

Malamin addinin ya bayyana abubuwa da halayen da ake bukatar matar dan sa ta mallaka

Kamar yadda ya yi wallafar wacce ta samu tsokaci fiye da 1,900, cikin halayen da ya ke bukata ya ce matar ta kasance musulma ta kwarai wacce ba ta aikata haram.

Hakazalika, ba ta ta’allakar da rayuwar ta wurin wadaka da shagulgulan duniya ba, ta kasance ta na da digiri a wanni fanni na musulunci, ta iya turanci kwarai, za ta iya zama a Malaysia da sauran su.

Naik ya wallafa wasu daga cikin abubuwan da dan sa ya mallaka da kuma bayanai a kan mahaifiyar Fariq da shi kan sa mahaifin da ‘yan uwan sa.

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari