Gwamna El-Rufa'i ya yi alkawarin magance matsalar tsaro a Jos da Kaduna


Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da takwaransa na jihar Filato, Simon Bako Lalong, sun yi alkawarin hada kai da rundunar Operation Safe Haven (OPSH) da sauran hukumomin tsaro don magance matsalolin tsaro da ke addabar jihohin biyu.

Sun yi wannan alkawari ne ranar Lahadi 5 ga watan Satumba lokacin da El-Rufai ya ziyarci Lalong don jajantawa gwamnati da mutanen jihar Filato kan hare-hare da kashe-kashen da aka yi a wasu sassan jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna El-Rufai ya ce:

“Filato da Kaduna ba makwabta ne kawai ba. Muna da dangantaka mai karfi kuma tun lokacin da muka hau mulki a 2015, ni da Gwamna Lalong muna tuntubar juna; Gwamna Lalong ne ya gabatar da mu ga Cibiyar Tattaunawar Ba da Agaji, wata kungiya mai zaman kanta ta duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya.

“Gwamna Lalong ne ya gabatar da ra’ayin cewa ya kamata jihohin biyu su kafa hukumomin gina wanzae da zaman lafiya.

"Filato tana da Hukumar Wanzae da Zaman Lafiya kuma Kaduna tana da Kwamitin Zaman Lafiya, muna aiki tare domin mun fahimci cewa jihohin mu biyu suna da girma kuma gidaje ne ga mutane da yawa a fadin Najeriya.

“Har sai idan mun inganta zaman lafiya tsakanin mutane daban-daban, sabanin haka rikici ba zai shafi jihohin biyu kadai ba har ma da kasar baki daya. Dangane da rikicin baya-bayan nan tsakanin Irigwe da Fulani, muna da Irigwe a Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna.

"Muna kuma da Ganawuri da Atakar a sassan Kudancin Jihar Kaduna, mu mutane daya ne kuma dole ne mu hada kai mu hada kan mutanen mu don mu zauna lafiya".

Lalong, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Farfesa Sonni Tyoden, ya ce hada kai tsakanin jihohin biyu zai dakile barazanar tsaro da ke fuskantar su.

Lalong ya jinjina wa El-Rufa’i bisa zuwansa don jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Filato kan rikice-rikicen da ke faruwa a jihar.

A bayanansa:

“Gaskiya ne Filato da Kaduna ba makwabta ne kawai ba, alabashshi suna da tarihi na dogon lokaci, don haka abin da ya shafi Filato ya shafi Kaduna kuma abin da ya shafi Kaduna ya shafi Filato.

“A wannan lokacin bakin ciki, zai saukaka lamurra lokacin da abokai masu tunani iri daya suka zo don magance matsalarsu. Muna godiya da nuna kawancen ku, muna godiya da tausayawar ku.".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN