Duba jerin manyan jihohi 10 da suka fi yawan kwararrun likitoci a Najeriya - Rahotu


Kwanan baya, kafofin yada labarai sun ruwaito ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige yana cewa Najeriya, Najeriya a matsayinta na kasa mai tasowa, da wuya ta cika ka'idar Majalisar Duniya da kuma kimar Hukumar Lafiya ta Duniya na samar da likita daya ga marasa lafiya 600.

A bangare guda kuma, ministan ya dage kan cewa Najeriya na da isassun likitocin da za su kula da mutane, yana mai cewa matsalar likitocin ita ce ba a turawa da rarraba ma'aikatan kiwon lafiya daidai gwargwado a wuraren da suka dace.

Ya ce yawancin likitocin kasar nan basu son aiki a yankunan karkara, sun zabi yin aikinsu a birane irinsu Abuja, Legas da Fatakwal.

Baya ga kwararrun likitocin cikin gida, Ngige ya ce likitocin da aka horar daga kasashen waje suma suna dawowa Najeriya don yin aiki.

Ministan ya yi ikirarin cewa a yanzu Najeriya tana da likitoci "kusan 4000 da 'yan kai”, inda ya dage cewa rashin kwararrun likitoci na da nasaba da rashin daidaita aikin.

Yace:

“Don haka, kusan kowa ya tafi Abuja, Legas da Fatakwal don zama. Kuma muna da cibiyoyin kula da lafiya na farko 10,000 wadanda aka yi watsu da su kamar yadda aka yi a kidaya ta karshe.”

Abin da alkaluma suka ce

A watan Agustan 2021, Ofishin Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar da rahoton kididdigar shekarar 2020 kan mata da maza a Najeriya.

Daya daga cikin muhimman kididdiga da aka dauka a cikin rahoton shine adadin likitoci a kowace jaha na tarayya (gami da yawan mata daga cikinsu).

Bayanan da Legit.ng ta samu, sun samo asali ne daga Majalisar Likitocin Hakori ta Najeriya.

Manyan jihohi 10 mafiya yawan manyan likitoci (alkaluman 2019)

Lagos - 2561

FCT - 2523

Ribas - 917

Oyo - 772

Edo - 727

Kaduna - 711

Kano - 632

Delta - 554

Anambra - 552

Filato - 538

Sauran jihohin Najeriya

Osun - 536

Enugu - 491

Ogun - 478

Kwara - 446

Borno - 377

Bayelsa - 359

Benue - 332

Cross Riba - 330

Imo - 319

Ondo - 293

Abiya - 289

Gombe - 286

Akwa Ibom - 278

Katsina - 266

Ekiti - 261

Nasarawa - 258

Bauchi - 243

Kogi - 218

Neja - 217

Sokoto - 201

Ebonyi - 184

Adamawa - 147

Kebbi - 144

Zamfara - 137

Yobe - 133

Jigawa - 131

Taraba - 86

Rahoton ya ci gaba da nuna cewa, tun daga shekarar 2019, Najeriya tana da likitoci 6,713 da ba a tantance su a karkashin kowace jiha ba. Adadin likitocin a kasar ya kai 24,640.

Sai dai, wani rahoto na baya-bayan nan da aka baiwa Hukumar Kula da Lafiya ta Najeriya ya bayyana cewa kusan likitoci 35,000 ne ke aikin a Najeriya.

Rahoton ya ci gaba da bayyana cewa, likitocin da ke aiki 35,000 suna cikin jimillar likitoci 80,000 da suka yi rajista da Hukumar Kula da Likitoci ta Najeriya (MDCN).

Wasu da ba sa aiki a Najeriya ana kyautata zaton cewa suna aiki a kasashen waje yayin da kadan daga ciki suka sauya sana'o'i.

Talauci: Rahoto ya nuna 'yan Najeriya miliyan 27 ke samun kudin shiga N100k a shekara

A wani labarin, wani rahoton Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama da Tattalin Arzikin Kasa (SERAP) ya ce ‘yan Najeriya miliyan 27 ne ke samun abin da bai kai Naira 100,000 ba a shekara, inji TheCable.

Kungiyar, a ranar Alhamis 2 ga watan Satumba, ta kaddamar da rahoto mai taken ‘Annobar da aka Manta da Ita: Yadda Cin Hanci da Rashawa a bangaren Lafiya, Ilimi, da Ruwa ke jefa 'yan Najeriya cikin talauci.'

A cewar rahoton, ‘yan Najeriya miliyan 56 na fama da talauci kuma 57.205 daga cikinsu galibinsu na dogaro da kansu ne.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN