Duba jerin jihohin da ke cikin barazanar kaɗawar iska mai karfi da ambaliyar ruwa a Najeriya


A ranar Litinin ne wani hasashen yanayi na BBC ya nuna cewa, mai yiwuwa ne ƙasashen Afirka ta yamma ciki har da Najeriya su fuskanci kaɗawar wata iska da ba a saba ganin irinta ba cikin kwana uku daga wannan Talatar har zuwa Alhamis.

Hasashen, wanda ita ma Hukumar kula da yanayi ta Najeriya Nimet ta tabbatar da shi na cewa, yanayin zai iya zuwa da mamakon ruwan sama, wanda ka iya haddasa ambaliyar ruwa da iska mai ƙarfi.

Iskar wadda za ta taso daga ƙasar Chadi, za ta ratsa ta arewacin Najeriya ta buga har zuwa ƙasar Senegal.

Hasashen ya ce ruwan saman zai haifar da mummunan yanayi na ambaliya a yankunan na yammacin Afirka.

Yaya yanayin zai kasance a Najeriya?

Shugaban hukumar kula da yanayi ta Najeriya, wato NIMET Farfesa Mansur Baƙo Matazu, ya shaida wa BBC cewa jiohin da ake hasashen za su fuskanci wannan ambaliya sun hada da Bauchi da Kano da Katsina da Zamfara da Kaduna da Kebbi da Sokoto da Neja.

Farfesa Baƙo ya ce a ranar Laraba jihar Zamfara da Kebbi da wani ɓangare na Sokoto za su samu ruwan sama mai karfi da iska.

Sannan a ranar Alhamis ana saran lamarin zai shafi Jihar Taraba da Filato da ɓangaren kudu wajen Enugu da kuma jihar Legas.

Farfesa Baƙo ya ce ana samun wannan yanayi ne sakamakon sauye-sauye na damuna wanda dama yawanci a farkon damina ruwan na zuwa babu karfi, sannan sannu a hankali zuwa karshen damina ruwa na karuwa.

Sannan ya ce ana cikin yanayi na iska mara karfi da ake kira 'low pressure' a Turance, to yanzu yanayin da ake ciki ana yawaita samun haɗuwar hadari da ruwa mai karfi.

Kuma yanayi a yanzu ya kai maƙura har maki 23 a ma'aunin salshiyas a makonnin da suka wuce, sannan a yanzu da damina ke zuwa karshe yana kai wa maki 18.2 zuwa 17.2.

Kasashen Afirka da iskar za ta shafa

Farfesa Baƙo ya ce baya ga Najeriya kusan duk ƙasahen Afirka ta Yamma kama daga Togo da Burkina faso da Saliyo da Gambiya da Senegel duk za su fuskanci wannan yanayi.

Me ya kamata mutane su yi?

A tattaunawar da BBC ta yi da Farfesa Adamu Tanko, kwarare kan muhalli da sauyin yanayi a Jami'ar Bayero, ya ce akwai bukatar mutane su kasance suna sanya ido da rage wasu dabi'u.

Farfesa Tanko ya ce irin wannan yanayi ba abu ne da za a iya daukar wani mataki ko yin wani abu na daban ba, sai dai Farfesa ya ce ana iya yin wasu abubuwa kamar su kasance masu lura da yanayi kafin a fita.

A kowacce shekara hukumomin kula yanayi na hasashen yadda damuna za ta kasance, da yawan ruwan da ake sa ran samu gami da yankunan da ake sa ran samun amabliya.

Su ma masana kan yi gargadi kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa da jan hankalin mutane kan matakan kare muhallansu.

A bana ma dai akwai hasashen cewa a jihohi da dama na Najeriya za a iya fuskantar matsalar ambaliyar ruwa, sanadiyyar ruwan sama da kuma cika da batsewar koguna da tafkuna, inda tuni ma wasu yankunan suka fara fama da ambaliyar.

A Najeriya da ke da yawan al'umma sama da miliyan 186 a kullum ana fargabar karuwar al'ummarta da kuma rashin tsare-tsare masu inganci da za su kare unguwannin biranen.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN