Duba abin da masana suka ce kan toshe layukan salula a Zamfara


Masana a Najeriya na bayyana damuwa kan matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na toshe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammaci.

Tun a daren Juma'a aka toshe layukan salula a fadin Zamfara, daga cikin matakan da hukumomi suka ɗauka na ƙoƙarin magance matsalolin taro a jihar.

Hukumar kula da kamfanonin sadarwa na Najeriya NCC ta tabbatar wa da BBC cewa ta katse layukan salula a Zamfara bisa umarnin gwamnati.

Mutanen jihar Zamfara sun wayi gari layukansu a toshe, ba su iya kiran waya, ba a iya kiransu kuma ba su iya aika saƙo da samun damar yin musayar sakwanni ta kafofin sadarwa na intanet.

Matakin toshe layukan na salula na zuwa ne bayan ɗaukar sabbin matakan tsaro a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna da suka haɗa da hana cin kasuwar mako-mako da takaita sayar da fetur da dokar hana fitar dare a fadin Zamfara da kuma rufe makarantu.

Sai dai masana harkokin tsaro kamar Malam Kabiru Adamu na ganin cewa an sha ɗaukar irin waɗannan matakan amma ba tare kawo ƙarshen matsalar tsaron ba. Kuma toshe layukan sadarwar zai yi matukar tasiri ga jefa mutanen yankin cikin mawuyacin hali.

A cewar masanin duk da ya fahimci manufar gwamnati na ɗaukar matakan, amma ya kamata matakan su shafi yankunan da ke kan iyaka, domin ɓarayin za su iya amfani da layukan sadarwa na Nijar da ke makwabtaka da jihohin na arewa maso yammaci.

Haka kuma masanin ya ce ƴan bindigar za su iya amfani da hanyoyin sadarwa na tauraron ɗan adam da kuma intanet. Don haka suna da zaɓi na hanyoyin da za su yi amfani da su domin sadarwa, a cewarsa.

Sannan matakan a cewar masanin za su shafi tattalin arziki da jefa jama'a cikin wahala.

Amma nasu ɓangaren hukumomi na jihohin da matsalar ta shafa sun ce ba gaba gaɗi suka ɗauki matakan ba, kamar yadda kwamishinan tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya ce "ba kwasan karan mahaukaciya ake yi ba, dubaru ne da ake dauka don ganin an dakile matsalar tsaro."

Sai dai Masanin tsaron Malam Kabiru Adamu ya shaidawa shirin Ra'ayi Riga wasu matakai da yake ganin ya kamata a gyara bisa ga waɗanda aka ɗauka tun da farko, kamar haka:

Mataki na farko a cewar masanin, ya kamata a tafi a mamaye mafakar ɓarayin a dazukan da suke.

Kuma a yi ƙoƙarin karɓe makaman da ke hannunsu da kuma ɗaukar mataki na daƙile hanyoyin da suke samun makaman.

Idan ana son a samu nasara sai an hada kai da makwabtan ƙasashe kamar Nijar da ke makwabtaka da Zamfara da Katsina.

Ya ce dole sai an ɗauki mataki iri ɗaya a yankunan kan iyaka ta yadda za a toshe duk wata kafa da ɓarayin za su sarara, domin ƴan bindigar za su iya zuwa cin kasuwa yankunan na kan iyaka.

Ya kuma ce ya kamata gwamnatocin jihohi su yi aiki tare da majalisun jihohi domin goyon bayan matakan da aka ɗauka.

"Dukkanin matakan da aka ɗauka an san cewa jama'a za su takura, amma babu wani mataki da aka ɗuka kan yadda za a taimaki jama'a kan wahalar da za su shiga," in ji shi.

Ya ƙara da cewa akwai harakokin kasuwanci da kamfanoni da ke dogaro da sadarwa domin gudanar da harakokinsu. "Ya kamata gwamnati ta yi tanadi na tallafa masu kamar yadda ta bayar da tallafin korona."

Masalar ƴan bindiga masu fashin daji da satar mutane ta yi ƙamari a Zamfara inda kusan a kullum sai an kai hare-hare.

An shafe shekaru 10 ƴan bindiga masu satar mutane da shanu na addabar jihar Zamfara da makwabtanta.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle yayin da yake ganawa da shugabannin ƴan sanda a fadarsa a makon da ya gabata ya ce ƴan bindiga sun mamaye wasu ƙauyuka na Zamfara, inda ya nemi a kafa dokar ta-ɓaci a jihohin arewacin Najeriya.

Binciken wata ƙungiya mai zaman kanta ya nuna cewa ƙauyuka kusan 70 ne ƴan bindiga suka mamaye a jihar Zamfara.

Haka kuma ƙungiyar ta ce mutum 364 aka kashe daga watan Fabrairun 2021 zuwa watan Agusta a Zamfara. Ƙungiyar ta kuma ce a shekarar 2021 mutum 1200 aka yi garkuwa da su a jihar kuma kusan mutum 10,000 aka raba da gidajensu.

BBC Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN