Dan kasuwa a jihar Kebbi ya kara kudin hayan shaguna daga N60.000 zuwa N300.000, yan haya sun ruga zuwa fadar Sarkin Gwandu


Rahotanni daga jihar Kebbi sun yi zargin cewa Sanusi Olumbo dan kasuwa mai ginin shagunan sana'a Olumbo Plaza da aka fi sani da Bindawa a garin Birnin kebbi babban birnin jihar Kebbi ya kara kudin hayan shagunansa daga Naira dubu sittin  N60.000 a shgunan kasa zuwa Naira dubu dari uku N300.000 nan take.

Safin labarai na isyaku.com ya samo cewa wannan lamarin ya tayar wa masu sana'a a ckin shagunnan benen hankali. Lamari da ya sa yan kasuwa da ke da shaguna a benen suka garzaya zuwa Fadar Mai Martaba Sarkin Gwandu domin gabatar da korafinsu ranar Laraba 7 ga watan Satumba..

Sai da mun samo cewa Sanusi Olumbo, wanda ke zaune a garin Jega, ya dauki matakin kara kudin hayan shagunansa ne bayan ya bankado wata harkalla da ya yi zargin ana gudanarwa ba tare da sani ko izininsa ba duk da cewa shi ke da mallakin wannan kasuwar.

A shekarar 2017, wasu mutane da ke kasuwanci a Olumbo plaza, sun karbi hayan Plazar daga Sanusi Olumbo, lamari da ya sa sauraran masu haya a Plazar suke biyan kudin haya ta hannun wadannan mutane.

Tsari da ake zargin ya haifar da matsalolin zamantakewa, kwace shagunan abokan hamayyar kasuwanci tare da kirkiro wasu tsare tsare da ake zargin wadannan mutane sun yi su ne domin gallaza wa wasu mutane da ke kwabar su zuwa ga lamarin gaskiya.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari