Miyagun 'yan ta'adda da ake zargin mayakan Boko Haram ne a halin yanzu suna luguden wuta a Babbangida, hedkwatar karamar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe.
Wata majiya ta tabbatar da cewa a halin yanzu ana musayar wuta tsakanin dakarun sojin da ke wuri da 'yan ta'addan, Daily Trust ta wallafa
Daily Trust ta ruwaito cewa, kamar yadda yace, mazauna yankin da yawa sun dinga gudu tare da neman wurin tsira a dajikan yankin.
A halin yanzu muna dajika inda muka tsere domin gujewa mutuwa; Na tabbatar kana iya jin karar harsasai da harbe-harbe," majiyar tace.
Adamu Gidado, wani mazaunin Babangida, wanda ya kubuce zuwa garin Damaturu yayin da aka fara ruwan wutar, ya sanar da Premium Times cewa mazauna yankin sun tsere zuwa daji.
Gidado ya ce ya ga sojoji masu yawa sun dumfari Tarmuwa yayin da yake hanyarsa ta zuwa Damaturu.
"Jama'ar Babangida sun tsere zuwa dajika domin tsoro. Na ga sojoji sun tunkaru garin yayin da na ke juyawa zuwa Damaturu," Gidado yace.
Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cigaban inda tace "'Yan Boko Haram a halin yanzu suna musayar wuta da dakarun soji a Babbangida. Amma mun sake tura wasu sojojin masu yawa," majiyar tace.
Har a halin yanzu babu bayanai sosai game da harin.
Legit Nigerian
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI