Da duminsa: 'Dan gwamnan Kano AbdulAziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Goggo wajen EFCC


Hafsat Ganduje, Uwargidar gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ta ki amsa gayyatar hukumar EFCC kan karar zargin cin da rashawa da 'danta, AbdulAziz Ganduje, ya kai kanta.

Premium Times ta ruwaito cewa an gayyaci Hafsat Ganduje ranar Alhamis da ta gabata hedkwatar EFCC dake Abuja.

Abdulazeez ya kai mahaifiyarsa, Hafsat Ganduje, kara wajen EFCC ne kan zarginta da amfani da karfin mulki wajen tarawa kanta dukiya.

A cewar majiyoyi da suka ga takardar karar da Abdulazeez ya shigar, ya bayyana cewa wani mai gine-gine ya tuntubeshi don samun wasu filaye a Kano da dubban daloli da kuma N35m matsayin la'ada.

Premium Times ta ce ta samu labarin cewa Abdulaziz yace ya baiwa mahaifiyarsa kudin.

Majiyar tace:

"Bayan watanni uku, mutumin ya gano cewa filayen da yace a samar masa tuni an baiwa wasu mutane daban kuma ya bukaci a mayar masa da kudinsa."

Yayinda aka tuntubi mai magana da yawun gwamnatin jihar Kano, Mohammed Garba, ya bayyana cewa ba zai iya magana kan lamarin ba.

Source: Legit.ng

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE