Bayan an yi wa Amarya auren dole, duba abin da ya faru tsakaninta da maijinta cikin mako 3 da yin aure


Yansandan jihar Adamawa sun kama wata Amarya yar shekara 19 mai suna Rumasa’u Muhammed, a kauyen Wuro Yanka da ke karamar hukumar Shelleng bisa zargin kashe mijinta.

Yayin da yake tabbatar da aukuwar lamarin, DSP Sulaiman Nguroje, ya ce Amaryar ta kashe mijinta ne sa ilin da take tambayarsa cewa ya bata takarda ya sake ta.

Ya ce "An kama Amaryar ce ranar Litinin bayan ta kashe mijinta ai suna Muhammad Adamu mai shekara 35 bayan ta caka mashi wuka lokacin da take nema ya sake ta".

Ya ce"Bincike ya nuna cewa iyayenta sun tilasta ta auri majinta da ta kashe ne duk da yake bata sonsa. An daura auren ranar 6 ga watan Agusta". Inji Nguroje.

Wata majiya da ke kusa da iyalinta ya ce Amaryar ta bukaci mijinta ya sake ta cikin lumana amma sai ya ki, daga bisani ta fusata ta dauko wuka ta caka masa a ciki, lamari da ya yi sanadin mutuwarsa.

Kwamishinan yansandan jihar Adamawa Aliyu Alhaji, ya bayar da umarnin gurfanar da amaryar a gaban Kotu da gaggawa saboda ya zama darasi ga wadanda ke shirin aikata irin wannan laifi.

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE