Bayan katse layin tarho duba yanayin da mazauna jihar Zamfara ke rayuwa babu sadarwa


Mazauna jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana halin takura da suka shiga sakamakon katse layukan waya da intanet da hukumomi suka yi. Shafin BBC ya ruwaito.

Hukumomin kasar sun dauki matakin ne da zummar shawo matsalar 'yan fashin daji da ta addabi jihar.

Ɗumbin jama'ar Zamfara ne a yanzu suke kwarara zuwa maƙwabtan jihohi domin kiran abokan hulɗa da 'yan uwa ta wayar tarho, da sauran aikace-aikacen da katse hanyoyin sadarwa ta haddasa a jihar.

Bayanan da ke fitowa daga Zamfara na cewa harkokin banki sun tsaya cak, yayin da hada-hadar kasuwanci ta taƙaita, a wasu lokuta ma 'yan uwa kan shiga zullumi saboda rashin ji daga makusantansu da ke sassan jihar.

Wasu Zamfarawa da BBC ta zanta da su sun bayyana irin wahalar da suke sha tun ranar Juma'a da aka katse sadarwa, kafin su iya kiran waya ko hada-hadar kuɗi a bankuna.

A cewar wani mazaunin "tun daga Ɗansadau a ƙaramarar hukumar Maru na tafi Funtuwa a jihar Katsina don na yi hada-hadar kuɗi saboda rashin sadarwa."

Ita ma wata mai sana'a ta intanet da yanzu haka ta yi balaguro zuwa wata jihar, ta ce rashin sadarwar ya yi matuƙar illa ga cinikin da take samu.

"Harkokina na kasuwancin da nake yi yawanci ina yin su ne a soshiyal midiya. Nakan ɗora abun da nake sayarwa a Whatsapp da Facebook, ka ga wannan lamari ya shafi rayuwata sosai tunda ba ni da sabis ma to ta ina zan fara?"

A wani gefen kuma lamarin ya shafi waɗanda ke zaune a wajen jihar ta Zamfara amma saboda matsalar sadarwar ba za su iya jin halin da makusantansu ke ciki ba.

Amma duk da haka da dama sun ce idan har matakin katse sadarwar zai taimaka wa hukumomin fatattakar ƴan fashin daji, to suna maraba da hakan.

Gwamnatin Zamfara ta fitar da sanarwar cewa sojojin Najeriya sun yi luguden wuta a fitattun sansanonin ƴan fashin dajin da ke faɗin jihar

Bayanan hoto, Gwamnatin Zamfara ta fitar da sanarwar cewa sojojin Najeriya sun yi luguden wuta a fitattun sansanonin ƴan fashin dajin da ke faɗin jihar

A ranar Juma'ar da ta gabata ne hukumomi a Najeriya suka katse hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara a wani bangare na fatattakar ƴan fashin daji da suka addabi jihar.

Kuma kwanaki biyu bayan ɗaukar mataki ne gwamnatin Zamfara ta fitar da sanarwar cewa sojojin Najeriya sun yi luguden wuta a fitattun sansanonin ƴan fashin dajin da ke faɗin jihar.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari