Ba zan sake afuwa gare ku ba, gwamnan arewa ga ‘yan bindiga, ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyinsu


Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce gwamnatinsa ba ta da sha'awar tattaunawa da 'yan bindiga, lura da cewa sun yi watsi da damar da aka taba basu.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa ya bayyana a Gusau cewa maimakon haka, jami’an tsaro zasu fatattake su daga jihar.

Legit.ng ta tattaro cewa Matawalle ya bukaci mazauna yankin da su kasance masu hakuri tare da tallafawa sabbin matakan tsaro da aka sanya domin fatattakar 'yan bindiga da abokan aikin su don dawo da zaman lafiya a jihar.

Yace:

"Gwamnatina ba za ta sake yin afuwa ga 'yan bindiga ba saboda sun kasa rungumar shirin zaman lafiya da aka yi musu tun farko."

Jaridar The News ta kuma ruwaito gwamnan ya ce yawan hare-haren da rundunar tsaro ke kaiwa yan bindiga ya sa sun fara kokarin neman sulhu da gwamnati.

Ya ce wakilan ‘yan fashin sun sanar da shi cewa sun tuba kuma suna son tattaunawa da gwamnati.

Matawalle ya lura cewa wasu daga cikin 'yan fashin suna ficewa daga Zamfara zuwa wasu jihohi sakamakon sabbin matakan tsaro da gwamnatin jihar ta bullo da su.

Amma, ya gargadi 'yan siyasa kan ba da kowane irin tallafi ga yan fashi, yana mai jaddada cewa 'yan siyasa su ji tsoron Allah su daina sayan babura don rabawa mutane da su kuma, suke sayar wa yan fashi don ci gaba da ayyukansu na mugunta.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatin Zamfara za ta hukunta duk wani dan siyasa da aka kama da hannu a lamarin.

Jihar ta katse hanyar samar da abinci, da albarkatun man fetur da sauran muhimman kayayyaki ga 'yan bindigar a sansanin su.

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN