An kama wani kato bisa zargin yi wa yarinya mai shekara 4 fyade


Jami'an hukumar NSCDC a jihar Nassarawa sun kama wani mutum a garin Kiliga da ke karamar hukumar Lafia bayan ya keta budurcin wata yarinya mai shekara 4.

Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito cew, Kakakin hukumar NSCDC na jihar Nassarawa Jery Victor ya sanar da haka a shelkwatar hukumar da ke Lafia ranar Talata 7 ga watan Satumba. Ya ce rundunar ta kama Musa Jibrin Yahuza ne bayan mahaifiyar yarinyar ta shigar da kara kan abin da take zargin ya aikata wa diyarta.

Kakakin ya ce "Mahaifiyar yarinyar mai suna Fatima Ibrahim ta yi yunkurin yi wa diyarta wanka ne, amma sai ta gan jini yana fitowa Pant na yarinyar.

Nan take ta shiga da ita daki ta yi mata tambayoyi, yarinyar ta ce Azizee ne ya shiga da ita daki ya ce ta kwanta a gado."

Ya ce rundunar tana gudanar da bincike duk da cewa wanda aka kama ya musanta zargin da ake yi masa. Ya ce za su gurfanar da shi a gaban Kotu bayan sun sami rahotun binciken asibiti.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari