Mutane biyu da ake zargin sun halaka Abdulkareem Ibn Na’Allah, babban dan sanata Bala Ibn Na’Allah, sun ce sun sayar da motar sa naira miliyan 1, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Wadanda ake zargin, Bashir Muhammad mai shekaru 23 da Nasiru Balarabe mai shekaru 27 sun bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis yayin da aka kai su ofishin rundunar ‘yan sanda da ke Kaduna.
Kimar motar ya kai N9m
Kakakin rundunar, ASP Muhammad Jalige ya sanar da manema labarai cewa motar Abdulkareem ta kai kimar naira miliyan 9.
Yayin amsa tambayoyin manema labarai, daya daga cikin wadanda ake zargin, Balarabe, mazaunin Kawo ne a jihar Kaduna, ya ce sun sayar da motar a naira miliyan 1 a Katsina.
Balarabe ya yi amfani da kudin sa wurin siyan shinkafar kasar waje, amma jami’an hukumar fasa kwauri sun kama shi a iyakar kasa sannan su ka kwace shinkafar.
Daily Nigerian ta ruwaito ya ce:
“Na siya buhunan shinkafa 23 da nawa kudin amma jami’an fasa kwauri sun kwace."
Dayan matashin ya ce ba talauci bane ya sa shi aikata ta’addancin
Dayan, Muhammad, mazaunin layin Rabah dake Kaduna ya ce bai san mamacin ba sai ranar da su ka halaka shi.
Da aka tambayi Muhammad idan talauci ne ya sa ya aikata wannan laifin, ya ce iyayen sa suna iyaka kokarin su wurin wadata shi.
Sai dai Kakakin rundunar ‘yan sanda, Jalige ya ce a jamhuriyar Nijar suka sayar da motar, an dawo da ita Najeriya ne bayan sun daidaita da jami’an da ke tsaron iyakar kasa da kasa.
Makashin ÆŠan Sanata Na'Allah: Buhunan Shinkafa 23 Na Siya Da Kason KuÉ—i Na
A wani labarin mai alaka da wannan, Daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu wurin kashe Abdulkareem Na'Allah, dan Sanata Bala Ibn Na'Allah, ya ce ya yi amfani da kudin ne ya siya buhunan shinkafa, rahoton Daily Trust.
Ya bayyana hakan ne yayin da 'yan sanda suka yi holensa a ranar Alhamis a Kaduna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Nasiru Salisu, mai shekaru 27 a duniya, daya daga cikin wadanda ake zargin ya ce Bashir Muhammad, babban wanda ake zargin ne ya kitsa masa su aikata laifin.
Legit Hausa