An kama katti 3 da suka yi wa budurwa mugun aiki bayan sun sace ta, duba abin da suka yi


Rundunar tsaro ta farar hula NSCDC a jihar Nassarawa ta kama wasu mutane uku daga cikin mutum hudu da suka sace wata budurwa mai shekara 19  suka yi mata fyade sau da dama a jihar. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Kakakin hukumar NSCDC na jihar Nassarawa Jerry Victor, ya tabbatar wa manema labarai ranar Talata 31 ga watan Agusta .

Ya ce wadanda aka kama su ne Muntari AKA Uzor, 34, Dahiru Ibrahim, 29, da Isah Nasiru,31, ya ce cikon na hudu Kamalu ya tsere.

Budurwar ta ce Muhktar ya nemi ya rage mata hanya a motarsa Sharon na jigila lokacin da budurwar take kan hanyarta na zuwa gidan kawarta. Sai dai bayan ta shiga motar sai barci ya kwashe ta nan take.

Daga bisani bayan ta tashi ne sai ta gan kanta a wani waje da bata sani ba. Nan ne Muhktar ya yi mata fyade kuma abokansa suka dinga zuwa suna kwancjya da ita.

Rundunar ta tsananta neman cikon na hudu daga cikin wadanda suka yi mata fyade, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari