Yarbawa sun gargadi Obasanjo kan shiga fadan Sunday Igboho da gwamnatin Buhari


Wata kungiya mai suna Yoruba for One Nigeria Forum (YONF), ta nemi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ya janye kansa daga rahoton da ke cewa yana lallabin Jamhuriyar Benin don kare Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho daga fuskantar hukunci. Jaridar Legit ta wallafa.

Kungiyar a cikin wata sanarwa mai taken, 'Olusegun Obasanjo shine babban mai cin gajiyar Hadin kan Najeriya' wanda Seun Adebayo Lawal, shugabanta na kasa ya sanya wa hannu, ya ce kiran ya zama tilas duba da irin fa'idodin da tsohon shugaban kasa daga hadin kan Najeriya.

Jaridar The Cable ta ruwaito daga wata sanarwar da kungiyar ke martani ga jita-jitar da ake yada wa kan cewa Obasanjo na tsoma baki wajen kubutar Igboho, ya bayyana cewa:

Tarihin Najeriya, a halin yanzu ya tabbatar da al'ummar Yarbawa a matsayin manyan masu cin gajiyar hadin kan Najeriya tun samun 'yancin kai.

"Abin mamaki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo dan kabilar Yarbawa ne wanda ya fi kowa cin gajiyar duk wani abin da Najeriya ta samu na hadin kan ta.

"Obasanjo shi ne dan Najeriya daya tilo daga zuriyar Yarbawa wanda ya taba mulkin kasar nan a karkashin mulkin soja da farar hula.

"Me kuma Najeriya za ta iya yi masa ko al'ummar Yarbawa? Wadanne bukatu ne suka cancanci al’ummar Yarbawa da Obasanjo bai iya yi ba a lokacin da yake Shugaban mulkin soja da Shugaban kasa?

"Ba ya bukatar a tunatar da shi irin rawar da hadin kan Najeriya ta taka a lokacinsa, a matsayinsa na Soja da Shugaban farar hula, don haka, abin da ya kamata ya yiwa al’umma shi ne yin kira ga zaman lafiya, ingantawa da bayar da shawarwari ga Najeriya don hada kai guda daya.

Kungiyar Yarbawa ta bayyana dalilin da yasa Obasanjo ya shiga batun kame Igboho

Kungiyar Yarbawa ta Afenifere, ta tabbatar da cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya gana da shugaban Jamhuriyar Benin, Patrice Talon, don shiga tsakani a lamarin Sunday Igboho.

An tabbatar da ganawar tasu a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta, ta hannun mataimaki na musamman kan yada labarai ga Obasanjo, Kehinde Akinyemi, PM News ta ruwaito.

Akinyemi ya ce:

"Obasanjo yana Jamhuriyar Benin a ranar Litinin kuma ya gana da Shugaban kasa amma babu wanda ya san abin da suka tattauna."

Sai dai, Afenifere, a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, ta ce Obasanjo ya kutsa cikin lamarin Igboho ne saboda baya son a dawo dashi Najeriya daga jamhuriyar Benin.


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE