Yanzu yanzu: Taliban ta kwace mulkin Afghanistan ta nemi gwamnati ta yi saranda, shugaban kasa ya gudu (Bidiyo)


Daga karshe dai mayakan Taliban sun shiga Kabul babban birnin Afghanistan, kuma sun nemi gwamnati kasar ta yi saranda ba da wani sharadi ba.

Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito cewa shugabann kasar Afghanistan Ashrif Ghani ya tsere zuwa kasar Tajikistan inda ake kyautata zaton ya sami mafaka.

Wannan yana faruwa ne bayan kasar Amurka tare da takwarorinta sun janye sojinsu da suka girka har tsawon shekara 20 bayan mumunan harin 911 a 2001 kan kasar Amurka da aka zargi Osama bin laden da kitsawa tare da marawar Taliban da ke da mazauni a Afghanistan.

Bidiyon yadda Taliban suka shiga Birnin Kabul:

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari