Wasu mutum 7 Yan gida daya sun mutu a garin Umueze Umuakanu da ke karamar hukumar Umuahia ta arewa a jihar Abia.
Mai gidan mai suna Mr. Jessey ne ya sayo suyan kamar yadda ABN TV ta ruwaito.
Rahotanni sun ce bayan yan gidan sun ci suyan, sun kuma sha lemun kwalba, sai dai daga bisani sai suka fara yanke jiki suna faduwa.
Nan take 7 daga cikinsu suka mutu, yayin da matar Mr Jessey da dansa daya suka rayu a cikin mawuyacin hali. An garzaya da su zuwa Asibiti.