Yadda masu ibada suka bijirewa rusau kan Mujami'arsu ta Ekklesiyar Yan uwa a jihar Borno


Yan kwanaki da suka gabata, Gwamnatin jihar Borno ta rushe Mujami'ar Ekklesiyar Yan’uwa na Najeriya (EYN) a birnin Maiduguri na jihar Borno. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

An yi zargin cewa jami'an Borno Civilian task force da ke aiki tare da hukumar Borno Geographic Information Service (BOGIS) sun kashe wani mai zanga zanga dangane da rasau da aka yi wa Mujami'ar da ke shiyar Moduganari a birnin Maiduguri.
Rahotanni sun ce Gwamna Zulum ya bayar da umarnin cewa a gudanar da bincike kan zargin kisan.

Sai dai an sami bayyanar wasu hotuna a shafukan yanar gizo, wanda ke nuna masu ibada na Mujami'ar suna gudanar da ibadarsu a harabar rusashshen Mujami'ar. Wasu suna zaune a kan kujerun roba wasu har a kan rusassun bulo na Mujami'an suka zauna, yayin da Malamin Mujami'ar ke gabatar da addu'oi.
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari