Yadda mahaifiya ta kamu da soyayya da babban abokin danta mai shekara 16 har suka yi aure


Wata mahaifiya ta auri babban abokin danta mai shekara 16 bayan ta kamu da soyayya da shi. Yanzu sun shafe shekara 12 a zaman aure miji da matarsa.

Marilyn Buttigieg mai shekara 60, yar asalin garin Crawley, da ke yammacin Sussex, ta fara haduwa da mijinta ne, William Smith, mai shekara 31 bayan danta ya kawo shi gida bayan sun taso daga Makaranta a watan Yuli 2006.

A waccan lokaci, mijinta yana da shekara 16 da haihuwa.


Marilyn ta ce ta sha fama da tsana da tsangwama daga jama'a da makwabta, har wasu yan uwanta sun rabu da ita sakamakon zabin soyayyarta da William.

Ta ce ita bata da manufar lalata rayuwar William ko ta jawo masa asara. Marilyn mahaifiyar yara 7 ce.

Ta ce idan William Yana son ya sami zuri'a, ita bata da damuwa a kan haka.

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari