Yadda budurwa ta sheke saurayinta ta gudu da motarsa kirar Mercedes mai darajar N7m


Rundunar yansandan jihar Akwa Ibom ta kama wata budurwa bisa zargin kashe saurayinta.

Ana zargin wacce aka kama mai suna Lauretta ta kashe saurayinta ne kuma ta gudu da motarsa kirar Mercedes Benz 4matic da darajarsa ya kai N7m.

Bayanai sun ce saurayinta  da ta kashe mai suna Chukwuemeka shi kadai ne 'da ga iyayensa kuma mai sana'ar shigowa da kaya.

Kazalika isyaku.com ya samo cewa abokanshi ne suka same shi jina jina a mace a cikin dakinsa bayan duk kokarin da suka yi domin ya zo ya yi aikin karbar isowar kayakinsa daga kasar waje ya ci tura.

Sai dai bayan an yi amfani da na'urar Tracker na motar ne, sai aka gano motar tare da Lauretta a wani Otel kusa da inda lamarin ya faru tana holewa.

Kazalika rahotanni sun ce wacce aka kama diyar wani hafsan dansanda ne a Ogoja na jihar Cross River
Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN