Yadda aka kashe Musulmai 30 matafiya a birnin Jos da ke jihar Filato


An kashe aƙalla mutum 30 tare da jikkata wasu da dama a Jos babban birnin Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya. BBC Hausa ta wallafa.

Waɗanda lamarin ya ritsa da su matafiya ne kuma Musulmai da ke kan hanyarsu ta zuwa kudancin ƙasar daga Jihar Bauchi bayan sun halarci taron bikin sabuwar shekarar Musulunci.

Wasu mahara sun tare motocin da suke ciki a yankin Rukuba sannan suka rufe su da sara yayin da suke wucewa ta cikin birnin.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce mutum 22 aka kashe a harin.

Sai dai wani ɗan jarida da ya ziyarci asibitin yankin ya faɗa wa BBC cewa ya ga gawar mutum 30, yayin da wasu ke jinya. Akasarin mutanen na ɗauke da sara na adduna da sauran makamai a jikinsu.

Ya zuwa yanzu babu tabbacin abin da ya haddasa rikicin amma lamarin ya faru ne 'yan kwanaki bayan wani tashin hankali tsakanin Fulani makiyaya da kuma wasu manoma 'yan ƙabilar Iregwe.

Gwamna Simon Bako Lalong ya yi Allah-wadai da harin sannan ya gargaɗi "msu tayar da fitina da su guji yin hakan" saboda "gwamnati ba za ta lamunci tayar da hankali ba".

Da ma dai an shafe shekaru ana fama da rikicin ƙabilanci a Jihar Filato, wadda ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari