Wasu matsafa sun yi wa yar shekara 50 fyade, suka kasheta suka cire idanu da al'aurarta


Wasu matsafa sun kashe wata mata mai shekara 50 mai suna Mrs. Patience Komone, a garin Umeh da ke karamar hukumar Isoko ta yamma a jihar Delta.

Shafin isyaku.com ya samo cewa bayan kashe wanan mata, matsafan sun jefar da gangan gawar jikinta bayan sun cire idanunta da al'aurarta.

Matar wacce  aka fi sani da suna Pat, yar asalin garin Otughievwen ne da ke karamar hukumar Ughelli ta yamma, iyalinta sun yi shelar  cewa ta bace tun ranar Talata 27 ga watan Yuli bayan ta bar gida zuwa  garin Umeh inda take zuwa yin sarin Barkono da kayan miya kuma take sayarwa a hanyar Sapele.

Kwamishinan yansandan jihar Ari Muhammed Ali ya tabbatar da haka ranar 4 ga watan Agusta, ya ce an gano gawarta bayan ta fara rubewa a daji ranar Talata, bayan yansanda sun kama wani dan acaba mai suna  Onoriode Simon Akpoavirhi mai shekara 25 wanda shi ne ya dauke ta kan babur ranar da ta bace.

Ya gaya wa yansanda lokacin bincike cewa tare da hadin baki da wani mai gyaran takalma ne mai suna Akpoghene Shoemaker suka kashe matar bayan sun yi mata fyade. Ya ce sun kasheta ne da adda.

Ya ce wani mutum ne mai suna Lucky Daniel da ke garin Ohoro ya biya su N100,000 kuma ya ce su kawo masa sassan jikin dan adam wanda suka hada har da idanu da al'aura.
Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari