Tap di jan: Ministan Buhari Ya Fallasa Yadda Ake Sata Ta Karkashin Kasa a Mulkin Shugaba Buhari


Abuja - Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, yace ana sata amma sai dai a sirrince karkashin mulkin shugaba Buhari.

Amaechi yace gwamnatin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta fi kowace gwamnati kokarin kare dukiyar al'umma. Jaridar Legit ta ruwaito.

Ministan ya yi wannan furuci ne yayin da yake amsa tambayoyi a wata fira da ya yi da jaridar dailytrust.

Da aka tambayesa game da gwamnatin shugaba Buhari, Amaechi yace wannan gwamnatin ta fi kowace rike amanar dukiyar yan ƙasa idan aka kwatanta da sauran.

Shin ana satar dukiyar kasa a fili kafin yanzu?

Amaechi ya kara da cewa ba kamar a baya lokacin da zaka ga mutum ba shi da hanyar samun ko naira ɗaya amma ya zama miliyoniya.

A cewarsa kuma babu matakin da ake ɗauka kan irin waɗannan mutanen a baya, wannan ba zai taba faruwa karkashin Buhari ba.

Ministan yace:

"Ina son yan Najeriya su yi adalci, zaka iya fitowa fili ka saci kudi a wannan gwamnatin? ba wai ina maganar muna cin hanci bane ko ba mu yi."

"Mu ɗauka muna sama da faɗi da dukiyar kasa, shin zaka iya ftowa fili ka saci kuɗi a wannan gwamnatin? Amma a gwamnatin baya meke faruwa? a kan titi za'a yi sama da kuɗaɗen al'umma."

"Cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a gwamnatin baya, ta yadda bama ta tashi ake ba. Ba kunya zaka ga mutum yana wadaka da dukiyarsa a fili kowa na gani."

Ana sata a gwamnatin Buhari amma a sirrince

Amaechi ya kara da cewa a wancan lokacin ko me ka yi kuma ko nawa ka ɗiba babu wanda zai hukunta ka.

Yace:

"Zaka gansu ko shagon kafinta ba su mallaka ba amma sun zama biliyoniya, kuma ba su boye wa."

"Amma a wannan gwamnatin, idan zakai satar kuɗi, sai dai ka yi a sirrince. Ba wai ina nufin abu ne mai kyau ba, babban laifi ne da ake hukunta wanda aka kama."

"Amma a gwamnatin baya, zaka saci dukiyar yan kasa ba wanda zai ce maka uffan, in ma an kama ka ba abinda za'ai maka. Amma a mulkin Buhari, da zaran an cafke ka zaka fuskanci hukunci."

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN