Shugabannin Taliban sun fara komawa Afghanstan don fara mulki | isyaku.com
$ads={1}
Amurka ta ce za ta so ta ga Taliban ta cika alkawarin da ta yi na mutanta 'yancin dan adam, bayan da ta kwace Afghanistan, kafin ta san yadda za ta yi alaka da gwamnatin kungiyar, wadda shugabanninta suka fara komawa Afghanistan domin kafa gwamnati.

Amurkar ta bayyana hakan ne yayin da kuma aka bayar da sanarwar cewa shugabannin kungiyar kasashe mafiya karfin tattalin arziki, G7 za su gana a makon mai zuwa domin tattaunawa a kan manufa daya kan sabon shugabancin Afghanistan.

Amurkar wadda matakin da shugabanta Joe Biden ya dauka da ake gani ya kai ga halin da Afghanistan din ta samu kanta a ciki yanzu, na sauyin gwamnati, a sakamakon janye dakarun Amurkar, ta tsaya ta ga yadda salon mulkin Taliban zai kasance a wannan karon, kafin ta san irin alakar da za ta yi da sabbin shugabannin.

Kamar dai sauran manyan kasashe masu karfin tattalin arziki, Amurkar tana jira ne ta ga yadda Taliban din za ta yi dangane da alkawarin da kungiyar ta yi na kiyaye hakkin dan adam a shugabancin, kafin ta amince ko kuma ta kulla sabuwar kiyayya ko hamayya da ita.

Yanzu dai shugabannin kungiyar da ke gudun hijira sun fara komawa Afghanistan din domin kafa gwamnati.

Daya daga cikinsu shi ne wanda aka kafa kungiyar da shi, Mullah Abdul Ghani Baradar, wanda ya koma daga Qatar, inda ya shafe watanni yana jagorantar yarjejeniyar ficewar dakarun Amurka daga kasar

Taron jama'a sun rika kabbara suna maraba da shi, a lokacin da aka wuce da shi a mota daga filin jirgin sama na Kandahar, cibiyar kafa kungiyar kuma babbar tungarta.

Shugaba Biden ya kafe a kan matsayinsa na janye sojin Amurka wanda ya bayar da kafar da Taliban ta kwace mulki
Bayanan hoto, Shugaba Biden ya kafe a kan matsayinsa na janye sojin Amurka wanda ya bayar da kafar da Taliban ta kwace mulki
Bayan wata tattauanawa ta wayar tarho ne, tsakanin Shugaba Biden da kuma Firaministan Burtaniya Boris Johnson, aka bayar da sanarwar cewa shugabannin kungiyar kasashe masu karfin masana'antun ta G7 za su yi taro, amma ba na gaba da gaba ba, a mako mai zuwa domin tattaunawa da daukar matsaya guda a kan yadda alakarsu da shugabancin na kungiyar Taliban a Afghanistan za ta kasance.

Firaministan Burtaniya Boris Johnson ya tattauna da Shugaba Biden na Amurka kan matsayar da za su dauka kan mulkin Taliban din
ASALIN HOTON, PA MEDIA
Idan kungiyar ta Taliban ta ki tabbatar da wannan alkawari da ta yi na mutunta 'yancin mata da shugabannin tsohuwar gwamnatin kasar, mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na Amurkar Jake Sullivan - ya ce to daga nan zabi daya kawai da zai rage shi ne sanya wa gwamnatin takunkumi.

Daman tun a yanzu ma gwamantin Biden ta ce ta dakatar da hanyar fitar da kudaden gwamnatin Afghanistan da ke a Amurka, da suka hada da zinare na biliyoyin dala da aka ajiye a wani banki a New York.

Kungiyar ta Taliban ta ce a karkashin shugabancinta mata za su iya karatu da yin aiki, amma bias tanadin dokokin Musulunci, sai dai me hakan ke nufi a aikace shi ne ba a sani ba.

Mata za su iya samun damar yin zabe, ko rike wani mukami na siyasa? Za su iya zama masu shari'a ko 'yan wasan motsa jiki? Babu wannan amsa zuwa yanzu.

Zabihullah Mujahid
Bayanan hoto, Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid a taron manema labarai na farko bayan karbe gwamnatin Afghanistan
Ko da aka matsa wa kakakin kungiyar Zabihullah Mujahid a lokacin wani taron manema labarai kan ya bayar da karin bayani a kan wadannan tambayoyi, sai ya nuna cewa sabuwar gwamnati da za ta zo da sabbin dokoki ita ce ke da wannan amsa.

Sai dai ya nuna cewa za a bukaci mata a fannin kula da lafiya da shari'a da ilimi da kuma aikin tabbatar da doka.

Harwayau a nan din ma a wana matsayi matan za su kasance, bai fayyace ba.

Duk da yadda wasu mata da sauran 'yan kasar ke nuna shakku kan batun tabbatar da 'yancin matan da kungiyar ta yi, wasu matan abin mamaki sun yi maraba da abubuwan da kungiyar ke fada, inda wata mata ta ce: ''Idan har za a ba su damar yin aiki da kuma karatu, ai wannan shi ne 'yanci a wurina, wannan ita ce iyaka. Wadda Taliban ba ta tsallaka ba zuwa yanzu...''

Rahotun BBC Hausa
Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN