Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sako Daliban Makarantar Bethel Baptist Kaduna



Yan bindiga sun sako ɗaliban makarantar sakandiren Bethel Baptist guda 15, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Idan zaku iya tunawa a bayan yan bindiga sun sako ɗalibai 28 daga cikin waɗanda suka sace ranar Lahadi 25 ga watan Yuli bayan an biya miliyan N50m kuɗin fansa.

Barayin sun sace adadin ɗalibai 121 a makarantar kamar yadda shugaban Baptist reshen Kaduna, Ishaya Jangado, ya bayyana, wanda shine ke jagorantar makarantar.

Shugaban ƙungiyar kiristoci ta kasa (CAN) reshen jihar Kaduna, John Hayab, yace yan bindigan sun sako ɗaƙibai 15 ranar Asabar da daddare, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Cikakken bayani zai biyo baya

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN