Shugaban kasar Afghanistan ya gudu zuwa kasar Tajikistan saura kiris Taliban ta kama birnin Kabul


Shugaban kasar Afghanistan Ashrif Ghani ya fice daga kasar Afghanistan zuwa makwabciyar kasar Tajikistan yayin da saura kiris mayakan Taliban su kama
Kabul babban birnin Afghanistan kamar yadda wani babban jami'in gwamnati Abdallah Abdallah ya sanar. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Wannan yana zuwa ne bayan mayakan Taliban sun kewaye Birnin Kabul bayan sun kama Larduna 26 daga cikin 34 na kasar a kasa da mako biyu kacal.

Mun samo cewa Kakakin Taliban ya ce sun ba mayakansu umarnin cewa kada su cutawa kowa. Ya ce kuma za a bar duk wanda ke son ficewa daga birnin ya yi haka cikin sauki. Ya ce Taliban za ta shiga birnin ne domin ta hana sace sacen dukiyar jama'a da mayar da doka da oda a cikin Kabul. 

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari