Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hallaka dan Sanata Bala Na'Allah da aka yi


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana “matukar bakin ciki” bayan kisan Kyaftin Abdulkareem, dan farko na Sanata Bala Na’Allah a jihar Kaduna, Leadership ta ruwaito.

A karshen makon nan ne wasu 'yan ta'adda suka shiga dan sanatan, inda suka daure shi da igiya suka makure shi har ya mutu.

Jama'a da dama sun bayyana jimami da mutu Abdulkarim, wanda ya kasance matukin jirgin sama kuma mazaunin jihar Kaduna.

Mutuwar Abdulkareem wani abu ne mai ban tsoro a cikin kalubalen tsaron da muke fuskanta a yanzu, amma ina tabbatar wa 'yan Najeriya cewa jajircewata ta kare rayuka da dukiyoyin dukkan 'yan Najeriya na nan daram."

"Ina bakin cikin rashin Abdulkareem da sauran wadanda tashin hankali ya rutsa da su kuma ina fatan yin kira ga 'yan Najeriya da su taimaka wa jami'an tsaron mu da bayanan sirri domin bin diddigi da gurfanar da wadannan gungun 'yan ta'adda a gaban shari'a,."

Masu ba tsageru bayanan sirri suna cutar da al'ummarsu ne kawai

A cewar Shugaba Buhari:

“Nazarin dan adam yana da mahimmanci ga kokarin shawo kan wadannan masu aikata laifuka; wadanda ke aiki a matsayin masu ba da bayanai ga masu aikata laifuka suna lalata al'ummominsu don jin dadin kudi."

A karshe shugaba Buhari ya yi addu'ar Allah ya jikan Abdulkarim Bala Na'Allah, kana ya mika ta'aziyyarsa ga Sanata Bala Na'Allah, in ji Tribune Nigeria.

Rahotun Jaridar Legit

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari