Saboda wata Mata magidanta biyu sun yi wa juna duka har da barnata motar dayansu


Wasu magidanta su biyu sun dambace kuma suka yi wa juna dukan tsiya har da barnata motar daya daga cikinsu saboda wata mata a Makurdi babban birnin jihar Benue. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Lamarin ya faru ne ranar Talata 31 ga watan Agusta 2021.

Wani ganau mai suna Atsuwe Shadrack, ya ce magidantan sun ba hammata iska ne saboda wata mata a kusa da babban kasuwar kasa da kasa a birnin Makirdi.

Sai dai bai yi bayani da musabba in lamarin ba. Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari