Saboda tsananin satar wata matar aure, ala tilas miji ya nemi Kotu ta raba aurensu


Wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.

Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito

Ya ce:

"Dukkan zaman sauraron shari'a da aka yi, wacce aka yi kara ta ki bayyana gaban kotu duk da cewa an kai mata sammaci sau da yawa.

"Don haka, kotun bata da wani zabi sai dai raba auren.

"Kotun ta tsinke ingiyar auren da ke tsakanin Mutiu da Aliyah Bamgbose a yau.

"Daga yau, ba matsayin mata da miji ku ke ba.

"Kowa ya kama gabanasa ba tare da cin zarafin juna ba; kotu na muku fatan alheri a duk abin da za ku yi a nan gaba."

Mr Kolawole ya bawa wacce aka yi kara ikon rike yayansu tagwaye mata ya umurci Bambgose ya rika biyan N10,000 duk wata kudin abincinsu.

Ya kuma bawa wanda ya yi karar ikon rike dansu namiji.

Mata ta ta fitine ni da sata

Bamgbose ya ce: "Mata ta barauniya ce, bata taba gamsuwa da abin da na ke bata, a kullum sace min kudi ta ke yi.

"Wanda ya fi min zafi shine lokacin da ta sace min Naira miliyan 3 ta bannatar.

"Saboda halinta, na fara ajiye kudi a rufin gidanmu amma duk da haka tana shiga ta sace.

"Da na gaji sai na bude asusun ajiya a banki hakan ya fusata ta ta fara gallaza wa rayuwata.

"Bisa dukkan alamu kudi na ta ke so ba ni ba."

Mata na tana bin maza a unguwan mu

Bamgbose ya kuma zargi matarsa da bin maza masu aure a unguwarsu. Ya ce ya yi wa wasu mazajen gargadi su dena harka da ita amma bata dena ba.

Daga bisani ta kwashe kayan gidansa ta tsere da tagwayensu mata biyu da bar masa yaro na miji.

Ya kuma kara da cewa tana bin bokaye don ya taba ganin laya a gidansu kuma ta gaza yin bayyanin inda ta samo shi.

Rahotun Jaridar Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN