Rikici na ƙara ƙamari a jam'iyyar APC a Kano


Jam'iyyar APC a jihar Kano da ke Najeriya na ci gaba da fama da rikicin cikin gida, wanda ake alaƙantawa da zabukan shugabannin jam'iyyar a matakin mazabu da aka gudanar a baya bayan nan.

Wani abu da ke sake fito da rikicin karara shi ne zaben shugabannin mazabu na jam'iyyar a daukacin jihohin Nijeriya 36 musamman ma jihar Kano ya bar baya da kura, sakamakon yadda zarge-zargen nuna wariya tsakanin yan jamiyyar wajen tsarin da aka bi kan yin zabe na mazabun ta hanyar tsarin masalaha.

Sakamakon yawaitar makamantan irin wannan koke ne dai daga wasu jihohin ne ya sa uwar jam'iyyar ta APC aikewa da wani kwamiti na sauraron korafe-korafe da bincike kan koken da wasu yan jam'iyyar ke yi kan zaben.

Kwanaki kadan da fara aikin kwamitin a Kano wasu daga cikin 'yan jam'iyyar ta APC a jihar irinsu Hon. Shaaban Ibrahim Sharada, dan majalisar me wakiltar kwaryar cikin birni suka zargi da mayar da su yan bora, ta hanyar kin karbar korafinsu kan zaben tare da amfani da yan banga wajen hana su shiga cikin harbar ofishin jam'iyya na Kano.

Sai dai Dr Kabiru Ibrahim, wanda shi ne shugaban kwamitin da uwar jam'iyyar APC ta aiko Kano domin saurarar koke kan zaben shugabancin jam'iyyar da aka gudanar na mazabu, ya musanta dukkan zargin nuna wariya ga yan jamiyyar a Kano.

Ya ce har ya zuwa yammacin jiya Laraba babu wani wanda ya zo gabansu ya ce yana da korafi, kuma su ba su ga wasu yan banga a harabar ofishin jam'iyyar na Kano ba.

Kazalika kalaman da uwar gidan Gwamnan Kano Hajiya Hafsatu Abdullahi Ganduje ta yi na cewar Kwamishinan KanananHhukumomi Murtala Sule Garo shi ne zai gaji mai gidanta a zaben na 2023 ya sake rura wutar rikici a jam'iyyar musamman ganin akwai wasu makusantan Gwamna Ganduje da ke neman kujerar.

Sai dai daga bisani gwamnatin Jihar ta musanta wannan magana.

Masu sharhi dai kan harkokin siyasa na da ra'ayin cewar ganin jihar Kano ce kan gaba wajen bai wa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari kuri'a sama da miliyan daya a lokacin zabe, wanda idan aka yi wasa wannan rikici da ya kunno kai ka iya shafar makomar siyasar Shugaba Buharin, da ma tasirin jam'iyyar a jihar da ma kasa baki daya.

Rahotun BBC Hausa

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN