Ofishin Ministan shari'a Abubakar Malami ya magantu kan zargin da ake wa Abba KyariBabban Lauyan Gwamnatin Tarayya, kuma ministan Shari'a Abubakar Malami, ya ce har yanzu ba ta karbi wata takarda a hukumance daga cibiyar binciken Amurka ta FBI ba da ke neman damar kame mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari.

Wannan ya fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga ministan, Umar Gwandu yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Punch.

FBI ta zargi Abba Kyari da karbar cin hanci daga hannun Hushpuppi, wani dan damfara dake fuskantar zaman kotu a Amurka, bayan kame masa wani abokin harkallarsa.

Allah Zai Wanke Abba Kyari, Hassada Wasu ∆≥an Sanda Ke Masa: Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin ‘Brekete Family’

Source: Legit.ng

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN