Mutane 146 sun mutu a jihar Kebbi sakamakon bullar cutar amai da gudawa a kananan hukumomi 20 cikin 21 a jihar


Sashen curutta masu saurin yaduwa a cikin al'umma a jihar Kebbi ya ce mutum 146 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar amai da gudawa (Cholera) a wannan shekara. Shafin labarai na isyaku.com ya wallafa.

NAN ta ruwaito cewa shugaban kwamitin kula da curuta masu yaduwa a cikin al'umma na jihar Kebbi Dr. Aminu Haliru Bunza ya gaya wa Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu haka ranar Talata a fadar Gwamnati da ke Birnin kebbi.

Dr Aminu ya ce an sami adadin wadanda suka kamu da cutar amai da gudawa guda 2.208 tsakanin watan Janairu zuwa Agusta.

Ya gaya wa Gwamna cewa tsakanin watan Janairu zuwa Agusta 2021, an sami bullar cutar amai da gudawa a kananan hukumomi 20 daga cikin 21 na jihar Kebbi. Ya ce daga cikin mutum 55 da aka yi wa gwaji, 26 sakamako.ya nuna cewa sun kamu da cutar.

Ya ce gaba daya a yanzu, mutum 146 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar a jihar Kebbi. Ya ce matukar mutum daya ya kamu da cutar a gari, za a dauka cewa an sami bullar cutar a garin. Ya yi Kira ga jama'a cewa su guji yin bahaya a waje yadda aka gan dama. 

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE