BBC Hausa ta ruwaito cewa kimanin mutum miliyan 4.4 ne ke rayuwa cikin matsananciyar yunwa a arewa maso gabashin Najeriya saboda hare-haren mayakan Boko Haram wadanda suka hana noma aiki, in ji Majalisar Dinkin Duniya.
Yankin dai na fama da matsalar tsaro na sama da shekara 20, MDD ta ce hakan zai iya kai wa ga rashin abin ci a yankin.
Mace-macen da aka samu sakamakon rikicin da kuma matsalar annobar korona sun ƙara ta'azzara lamarin.
Masu kai hare-hare dai sun fi kai wa manoma a yankin arewa maso gashin da nufin daƙile samar da abinci.
Bugu da ƙari hare-haren nasu na ƙarasa wa har kan jami'an tsaron Najeriya a yankin.