Me zai biyo bayan miƙa wuyan da ƴan ƙungiyar Boko haram suke yi a Borno?


A baya bayan nan ana ci gaba da samun labaran da ke nuna yadda wasu mayaƙan ƙungiyar Boko Haram suke miƙa wuya ga hukumomi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

A yayin da waɗannan mayaƙa suke miƙa wuya bayan da suka yi ikirarin tuba daga kai hare-hare, lamarin ya jefa shugabannin jihar Borno cikin tsaka mai wuya kuma ya sa masu sharhi suna yin kira da makukunta su yi kaffa-kaffa kan karbarsu.

A gefe guda, ana ganin miƙa wuyan na ƴan Boko Haram a matsayin wata alama ta kawo ƙarshen yaƙi da ƙungiyar mai da'awar kafa Daular Islamiya a Najeriya ta shafe shekaru 12 tana yi.

Sai dai kuma a wani bangaren ana fargabar hakan ka iya zama kitso da kwarkwata idan aka yi la'akari da yadda wasu da suka taba tuba suka koma fagen daga.

A wata sanarwa da gwamnatin Borno ta fitar a ƙarshen mako, gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce karɓar ƴan Boko Haram da suka tuba yana tattare da hatsarin fusata waɗanda rikicin ya shafa kamar yadda tubabbun ƴan Boko Haram za su iya shiga ISWAP idan aka ki karɓarsu.

A cewar gwamnan "mu da muke jihar Barno, muna cikin mawuyacin hali bisa miƙa wuyan da mayaƙan Boko Haram ke yi. Yanzu dole ne mu zaɓi cikin abu biyu masu muni: wannan yaƙin da ya ki ci ya ƙi cinyewa da kuma rungumar waɗannan ƴan ta'addar da suka miƙa wuya suke so su dawo cikinmu."

Ya ce a jihar akwai mutane da dama da ƙungiyar Boko Haram ta kashe wa ƴan uwa kuma har yanzu suna cikin alhinin mutuwarsu, don haka zai yi wuya su iya rungumar mayaƙan masu miƙa wuya har su iya rayuwa tare da su a wuri guda.

"Ko sojoji ma, wannan abu ne mai wuya a gare su saboda akwai abokan aikinsu da ƙungiyar ta kashe. Babu wanda zai iya rungumar makashin masoyinsa hannu bibbiyu," in ji Zulum.

Ya ce lamarin na buƙatar kulawar masu ruwa da tsaki da wakilan al'ummomi su hada kai wajen tabbatar da cewa an samo mafita.

Gwamna Zulum ya ce zai tattauna da Shugaba Muhammadu Buhari da manyan hafoshin tsaro da shugabannin al'umma da malaman addini da ƴan majalisar wakilai da malaman makaranta da sauran masu ruwa da tsaki musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa don ganin an samo mafita a wannan lamari.

Babu zaɓi mai sauƙi'

Duk da Farfesa Zulum ya ce zai tattauna da Shugaba Buhari da kuma masu ruwa da tsaki a Borno domin samun mafita amma kuma bai bayyana tsari ko matakan da gwamnatinsa za ta bi ba.

Sai dai masana al'amurran tsaro a Najeriya kamar Group Captain Sadiq Garba Shehu (mai ritaya), ya shaida wa BBC cewa shiga tsaka mai wuya ba abun mamaki ba ne idan aka yi la'akari da yanayin yakin Boko Haram.

Masanin ya ce ko wane yaƙi yana da yanayinsa domin akwai yaki na ƙasa da ƙasa akwai kuma yaƙi wanda yan kasa ke faɗa da gwamnatin kasarsu.

A cewar Captain Sadiq, yaƙi na kasa da kasa tsarinsa ya fi saukin kawo karshensa domin idan an gama yaƙi kowa zai koma ƙasarsa saɓanin na yan gida saboda waɗanda ake yaƙin da su ƴan ƙasa ne suna da ƴanci da iyaye da ƴan uwa.

"Irin wannan yaƙin haka yake ƙarewa tun da sojojin Najeriya ba su kashe ƴan Boko Haram gaba ɗaya ba. Ko dai masu tayar da ƙayar baya su gaji da yaki su ajiye makamansu ko kuma a kama su.

"Idan an kama su ko sun miƙa wuya, bisa dokar ƙasa da ƙasa ba za a iya harbe su ba domin zai iya zama aikata laifukan yaƙi, dole sai kotu ta tabbatar da laifinsu" in ji shi.

Masanin na tsaro ya ce ba shakka yadda mayaƙan ke miƙa wuya, alama ce da ke nuna cewa rikicin boko haram ya kawo ƙarshe.

Ya ce ya kamata gwamnati ta fahimci cewa ba duka mayaƙan ba ne suka fito suka miƙa wuya domin akwai waɗanda suke sauraren matakin da aka ɗauka kan waɗanda suka fito suka tuba wanda zai iya zama share fage gare su.

Idan kuma suka ji cewa ba za a karɓe su ba, sun san cewa za su ci gaba da tabbata a matsayin ƴan Boko Haram, a cewarsa.

Ya ƙara da cewa a ɗaya ɓangaren kuma akwai waɗanda aka kashe wa ƴan uwa da mazajensu an bar su da marayu - "don haka babu hanya mai sauki ta ƙare wannan yakin."

"Dole sai an saka haƙuri, domin duk yaƙi irin wannan na sunkuru sai an dawo kan yafiya da sulhu,"

Don haka ba wani zaɓi mai sauki - wannan tsaka mai wuya ce," in ji Group Captain Sadiq Garba Shehu mai ritaya.

Ina mafita?

Masanin na tsaro ya ce dokar yaƙi ta bayar da shawarar abin da ya kamata a yi, kuma a cewar Captain Sadiq akwai maganar duba batun yafiya amma ba kowa za a yafewa ba.

Ya ce akwai manyan yan Boko Haram akwai kuma waɗanda aka tilastawa shiga kungiyar musamman yara. Idan an diba an ga akwai manyan mayaƙan ƙungiyar da suka kashe mutane, a cewarsa bai kamata a yafe masu ba.

Masanin ya ce za a yin bincike a gano girman laifukan tubabbun a diba a ga ko za a karɓe su.

Amma waɗanda aka shiga da su da ƙarfi ana iya diba wa a yafe masu - "dokar ta diba irin wannan tsakar mai wuyar da za a shiga domin babu wanda zai fito ya yi saranda kuma a dirka masa bindiga."

Ya ce dole sai ko wane ɓangare ya saki wani abu an rungumi haƙuri.

Kuma a cewarsa gwamna Zulum ba ya son ya nuna cewa ga inda ya karkata amma shi ne ya sanar da kowa cewa karɓar tubabbun na Boko Haram da rashin karɓa ana tsaka mai wuya akwai bukatar a yi shawara.

"Ɗan Boko Haram idan ya san zai fito ba za a karɓe shi ko kuma za a kashe shi, to gara ya zama ɗan Boko Haram na har abada, ba wani dalilin yin tuba."

"Babu hanya mai sauƙi, dole sai an yi hakuri - kowa ya san ɓarnar Boko Haram, haka kuma ƴan ƙasa ne, suna da ƴan uwa kuma fitowarsu zai bayar da sa'ar kawo karshen yaƙin," in ji shi.

Ya kuma ce akwai waɗanda kotu ta wanke kuma ba wanda zai ce ba su da ƴancin yin walwala ko barin kasa, haka ma waɗanda suka fito gidan yari bayan sun gama zaman wa'adin da aka yanke masu.

Rahotun BBC Hausa

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE