Ku Tuba Ku Mika Makamanku Tun Kafin Mu Kariso, COAS Yahaya Ga Yan Boko Haram/ISWAP


Shugaban rundunar sojin kasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya yi kira ga yan ta'adda su tuba tare da mika makamansu, kamar yadda the cable ta ruwaito.

COAS Yahaya ya yi wannan kiran ne ranar Litinin a Maiduguri, jihar Borno yayin kaddamar da sabon shirin kula da jin dadin jami'an tsaro na haɗakar Operation Haɗin Kai.

Yan ta'adda nawa suka mika wuya a hukumance?

A cewar rundunar sojojin kasa a makwanni biyu da suka shude sama da yan ta'adda 100 suka tuba tare da mika makamansu ga jami'an tsaro.

A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Borno tace zata cigaba da baiwa masu tada ƙayar bayan kwarin guiwa domin su mika wuya.

Wane mataki sojoji zasu ɗauka kan masu taurin kai?

Da yake jawabi a wurin taron manjo Yahaya yace duk waɗanda suka ki mika makamansu zasu fuskanci fushin sojoji domin zasu iso garesu.

COAS Yahaya yace:

"Muna samun nasara suna tuba da mika makamansu kuma muna kira gare su da su cigaba da aje makamansu domin su rungumi zaman lafiya."

"Muna kiran sauran dake can cikin daji su fito su mika makamansu saboda mu karkare wannan matsalolin."

"Amma idan suka yi taurin kai, to zamu isa gare su kamar yadda muka kai ga wasu, zamu shiga daji ga waɗanda suka yi taurin kai suka ki mika wuya ko a Arewa-Gabas ko Arewa-Yamma ko Arewa-Tsakiya."

Yahaya ya yaba da haɗin kan da ake samu tsakanin sojoji da sauran hukumomin tsaro, inda ya kara da cewa ya fara haifar da ɗa mai ido.

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN