Kotu a Birnin kebbi ta tura uwa da uba Kurkuku bayan sun ce jaririn da suka haifa Annabi ne ya dawo


Kotun shari'ar Musulunci ta 1 da ke Nassarawa a garin Birnin kebbi, ranar Alhamis 26 gavwatan Agusta, ta tasa keyar wasu ma'aurata zuwa Kurkuku bayan sun yi ikirarin cewa dan da suka haifa Annabi ne. Shafin labarai na isyaku.com ya tattaro.

Mai gabatar da kara na yansanda Sgt Faruku Muhammad, mai lambar aiki 493010 ya gaya wa Kotu cewa "Ana zargin wadanda aka yi kara ne a gaban Kotu bisa tuhuma guda uku da suka hada da.

1. Hada Baki domin aikata laifi.

2. Tayar da hankalin jama'a.

3. Cin zarafin Addinin Musulunci.

Sgt Faruku ya ce, wani lokaci a baya kaɗan, a karamar hukumar Bunza, Aliyu Isah da matarshi Binta Isah sun ce dan da suka haifa Annabi ne"

Ya ce sakamakon haka lamarin ya tayar da hankalin jama'a a wannan yankin.

Kotu ta tambayi Aliyu Isah ko abin da ake tuhumarsa da aikatawa haka ne? Aliyu ya shaida wa Kotu cewa haka ne sun ce dan da matarsa ta haifa Muhammad Basiru Annabi ne.

Kazalika Binta Aliyu ta shaida wa Kotu cewa tabbas dan da ta haifa Muhammadu Basiru Annabi ne.

Ta gaya wa Kotu cewa Annabi Muhammad ne ya yi mata ishara da wahayi cewa za ta haifi Annabi tare da ce mata Manzon Allah zai dawo a cewar Binta.

Ta ce "Har yanzu ina magana da manzon Allah. Har da Nana Fatima ina magana da ita" inji Binta.

Ta gaya wa Kotu cewa "Lamarin  ya farune a garin Kamba, kafin su kaura zuwa Bunza bisa umarnin annabi".

Bayan mahaifan sabon "annabi" sun gama yi wa Kotu bayani, dansanda mai gabatar da kara ya ce:

" Ina rokon Kotu ta yi masu hukunci daidai da abin da suka aikata tunda sun amsa laifin tuhuma da aka yi masu, tunda wannan Kotun Addinin Musulunci ne, kuma Musulunci ya tabbatar mana da cewa bu wani Annabi da zai dawo".

Alkali Mu'awiyya Shehu Birnin kebbi, ya yi umarnin cewa a tasa keyar Aliyu Isah da Binta Aliyu zuwa Kurkuku har zuwa ranar Alhamis mai zuwa domin Kotu ta yanke masu hukunci.

https://www.facebook.com/isyakulabari/videos/1103834420148378/

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE