Kawar dan sanatan da aka kashe ta bayyana abubuwan da suka faru kafin mutuwarsa


Gidan da aka tsinci gawar Aldulkarim Bala Na'Allah a ranar Lahadi an ce a watanni biyu da suka gabata wasu tsageru sun afka gidan sun tafka sata a ciki, in ji rahoton Daily Trust. Jaridar Legit ta ruwaito.

Na’Allah, da gs Sanata Bala Ibn Na’Allah, mai wakiltar Kebbi ta kudu, an same shi daure yayin da wasu suka makure da igiya a ranar Lahadi a gidansa na Malali da ke Kaduna.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce maharan sun tsere da motarsa kirar Lexus SUV.

Da aka zanta da kawar marigayin wacce take abokiyar karatunsa a Makarantar Sakandaren 'yan sanda ta Minna, ta tattaro cewa sun yi takaitaccen hira na kiran bidiyo a yammacin ranar Juma'a kafin matukin jirgin ya gaya mata cewa yana da taron gaggawa da zai halarta.

Ta ce:

“Na kira shi a mun yi hira ta bidiyo a ranar Juma’a da yamma amma yayin zantawarmu, tirela ta wuce don haka ban ji shi ba sai na gaya masa cewa zan sake kiransa daga baya.

“Daga nan sai ya sake kirana a wannan ranar da misalin karfe 6 na yamma da sakanni cikin tattaunawar mu, zan tambaye shi meke damunsa saboda fuskarsa ta nuna damuwa amma sai ya fada min cewa yana da taron gaggawa kuma zai tafi ofishin NEPA sannan zai kira ni daga baya.”

An tafka barna a gidansa watanni biyu da suka gabata

Ta ce wannan shi ne lokaci na karshe da ta ji daga gare shi amma ta shaida cewa watanni biyu da suka wuce, matukin jirgin ya sanar da ita cewa an yi wa gidansa fashi inda aka sace masa wasu na’urori.

Ta kara da cewa:

"An kutsa gidan, sun fasa katangar gidan suka shiga falo daga abin da ya gaya min kuma na shawarce shi da ya bar yankin tunda ba shi da kwanciyar hankali amma ya gaya min cewa an sada shi da mai gadi."

Kawar tasa ta makaranta, wacce ita ma mazauniyar garin Kaduna ce yayin da take kuka, ta shaida wa wakilin Daily Trust cewa:

“Ya ce wani ya yaudare shi kimanin Naira miliyan 50.

"Ya bai wa wani kudi don ya canza masa su zuwa dala amma mutumin ya yaudare shi. Mutumin ya biya shi N15m amma karar tana kotu a Kano har yanzu.”

Ta bayyana marigayin a matsayin mutum mai tawali'u kana mai son cusa tarbiyya a tsakanin 'yan Najeriya.

Ta kara da cewa:

“Tazarar da ke tsakanin mu ba ta da yawa amma ya kasance yana min wasa yana cewa shi babana ne. Yana son mutane masu aiki tukuru wanda yana daya daga cikin dalilan da yasa muka shaku tun lokacin da muke makarantar sakandare.”

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN