Karin Bayani: Yadda Motar Kwastam Ta Kwace Ta Yi Kan Jama'a Ta Hallaka Mutum 15 a Katsina


Mutane sun fito zanga-zanga a garin Jibia, jihar Katsina, kan kashe wasu mutum 15 da jami'an kwastam suka yi yayin da suka biyo masu fasakwaurin shinkafa.

Wasu shaidu sun bayyana cewa mutane da dama sun samu jikkata kuma a halin yanzun suna gadon asibiti ana kulawa da lafiyarsu. Shaidun sun tabbatar da cewa wata motar jami'an kwastam ce ta yi kan dandazon mutane yayin da suka biyo wasu da ake zargin yan fasa kwaurin shinkafa ne a yankin.

Rahotan jaridar Aminiya ya nuna cewa a sakamakon haka mutum 10 sun mutu nan take, yayin da karin wasu biyar suka biyo baya.

Me ya jawo hatsarin?


Wata majiya da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa jaridar Premium times cewa:

"Sun biyo yan fasa kwauri cikin matsanancin gudu, direban ya kasa sarrafa motar ta yi cikin jama'a inda ta hallaka mutane da dama. Wannan shine dalilin zanga-zanga."

"Fusatattun matasa dake cikin masu zanga-zangar sun yi kaca-kaca da motar jami'an kwastam din."

Me hukumomi suka ce game da lamarin?


Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa, ya ce, ya zuwa yanzun ba shi da rahoto a kan lamarin, amma yana jiran rahoton DPO na ’yan sandan Jibia. Hakazalika, har zuwa yanzun hukumar kwastam ta ƙasa (NCS) ba tace komai ba game da lamarin da ya faru.

source Legit Nigeria

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE