Hotuna: An Gina gunkin Aisha Yusuf, duba abin da lamarin ya janyo tsakanin matasa


Wani matashi dalibi dan Najeriya mai suna Omoregie Emmanuel ya gina gunkin 'yar gwagwarmaya kuma 'yar kasuwa Aisha Yesufu. Jaridar Legit ta ruwaito.

Dandalin Just Event Online ta ba da rahoton cewa Omoregie ya gina gunkin a matsayin wani bangare na ayyukansa don kammala karatun digiri a fannin fasahar zane-zane na 'Fine and Applied Arts'.

Saurayin ya zabi ya gina gunkin A'isha ne domin yaba mata bisa gwagwarmayar da ta yi a 'yan kwanakin nan. Omoregie ya kaddamar da aikin gunkin a ranar Juma'a, 6 ga watan Agusta.

A cikin hotunan da aka yada a kafafen sada zumunta, gunkin ya nuna shahararren hoton Aisha yayin da yake daga tutar Najeriya a sama.
Jama'a sun yi ca wajen cece-kuce kan gunkin

Mutane da dama sun yi sharhi kan wannan gunki da matashi ya gina. Wasu na yabawa wasu kuwa na fadin hakan bai dace ba, tare da bayyana dalilansu

Awodeji Oluremi ya ce:

"Wannan abin a yaba ne, ina taya Aisha murna."

Yahaya Mohammed yayi sharhi, ya ce:

"Wannan ba al'adar Islama bane, haramun ne!"

Waheed Qodir ya rubuta:

"Ta cancanci hakan."

Khadeejat AbdulGaniy Olabisi ta ce:

"Gunki haramun ne a Musulunci."

Hoton gunkin Aisha Yesufu | Hoto: JUST EVEN ONLINE


Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari