Hotuna da bidiyon wankan 'Budan Kai' na Zahra Nasir Bayero, amaryar Yusuf Buhari


A rana ta hudu a farin cikin bikin dan shugaban kasa, Yusuf Buhari da 'yar sarkin Bichi, Zahra Nasir Bayero, an yi shagalin budan kai jiya Asabar 21 ga watan Agusta.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka daura auren Yusuf Muhammadu Buhari da ga shugaban kasar da Najeriya da kuma Zahra Nasir Bayero 'yar sarkin Bichi.

An yi budan kai jiya Asabar 21 ga watan Agusta, kuma Legit Hausa ta samo wasu daga cikin hotuna da kuma bidion shirin budan kai.
Kalli hotunan da bidiyo:
Hotuna da bidiyon wankan 'Budan Kai' Zahra Nasir Bayero, amaryar Yusuf Buhari

Lokacin da ake cabawa amarya Zahra kwalliya | Hoto: @tolabanks

Hotuna da bidiyon wankan 'Budan Kai' Zahra Nasir Bayero, amaryar Yusuf Buhari

Amarya bayan ta sha kwalliya | Hoto: @tolabanks

Hotuna da bidiyon wankan 'Budan Kai' Zahra Nasir Bayero, amaryar Yusuf Buhari

Yayin da amarya ta iso gidansu ango | Hoto: @tolabanks

Kalli bidiyo

Hotunan Aisha Buhari lokacin da take jiran isowar amaryar dan ta Yusuf Buhari

Kafin wannan budan kai, uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta watsa wasu hotunan manyan mutane da kawayenta da ke jiran karbar surukar ta, Zahra Nasir Bayero.
Aisha Buhari, da watsa hotunan a shafinta na Instagram ranar Asabar 21 ga watan Agusta ta ce:"
An shirya komai don maraba da karbar sabuwar 'yarmu cikin dangi."

An gan manyan iyayen biki, ciki har da uwargidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo, Madame Fatoumatta Barrow da wasu mata su masu fada a ji.
Rahotun legit
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari