Gwamnonin Jam'iyyar APC Sun Shiga Ganawar Sirri da Wani Tsohon Gwamna


Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja, ya gana da gwamnonin jam'iyyar APC uku a Ibadan, kamar yadda Punch ta ruwaito. 

Rahotun Jaridar Legit ya ce taron wanda aka shafe sama da awanni uku ana yinsa ya gudana ne a gidan Ladoja dake Ibadan, babban Birnin Oyo. 

Duk da cewa babu wani cikakken bayani game da abinda suka tattauna, amma ana tsammanin ganawar tana da alaÆ™a da sauya sheka zuwa APC. 

Wane gwamnoni ne suka halarci taron? 

Premium times ta ruwaito gwamnonin APC da suka halarci taron sun haÉ—a da, Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na APC. Sauran sun haÉ—a da gwamnan jigawa, Abubakar Badaru, da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu. 

Me aka tattauna a ganawar? 

Wata majiya ta shaidawa hukumar dillancin Najeriya (NAN) cewa gwamnonin sun je gidan Ladoja ne domin tattauna matsalar tsaro da kuma jawo hankalinsa zuwa APC. 

"Suna son ya sauya sheka zuwa jam'iyyarsu ta APC ne," inji wani makusancin É—aya daga cikin jiga-jigan siyasa, wanda ya nemi ya É“oye sunansa. A halin yanzun duk wani kokari na jin ta bakin Mr. Ladoja ko kuma gwamnonin na APC ya ci tura. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN