Duba wani mugun abu da yan bindiga suka dinga yi wa mata a Zamfara


Al'ummar Karamar Hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara a arewacin Najeriya sun tsunduma cikin wani mummunan tashin hankali bayan da 'yan bindiga suka rika yi wa matan yankin fyade. BBC Hausa ta ruwaito.

Wani da BBC ta yi hira da shi ya bayyana cewa gida-gida aka rika bin mata ana musu fyade, ciki har da matar da ta ki amincewa a yi lalatar da ita wadda yace ta riga mu gidan gaskiya.

Quote Message: A asibitin karamar hukumar tsafe na isko mata wadanda aka yi wa fyade daga Sullubawa an kai mata 9, daga unguwar Tofa an kai mata 6 sai kuma daga Makera da aka kai mata uku. Yanzu da kinje tsafe za ki ga mata suna tururwar barin yankin domin ba za su iya zama ana cin zarafinsu ba kamar haka.

A asibitin karamar hukumar tsafe na isko mata wadanda aka yi wa fyade daga Sullubawa an kai mata 9, daga unguwar Tofa an kai mata 6 sai kuma daga Makera da aka kai mata uku. Yanzu da kinje tsafe za ki ga mata suna tururwar barin yankin domin ba za su iya zama ana cin zarafinsu ba kamar haka.

Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce tun bayan kama wani mutum cikin Fulanin abin ya zama bala'i.

Quote Message: Babu jami'in tsaron da zai iya shiga daji inda wadaddan mutane suke, su da kansu 'yan fashin dajin ke cewa ba za a iya cimmusu ba.

Babu jami'in tsaron da zai iya shiga daji inda wadaddan mutane suke, su da kansu 'yan fashin dajin ke cewa ba za a iya cimmusu ba.

Ya kara da cewa ko a baya dama sukan yi wa mata fyade amma dai bai kai adadin da suke yi ba a yanzu.

Sai dai hukumomin asibitin da aka kai matan sun shaida wa BBC cewa "Mata bakwai kawai aka kai musu da wannan matsala" kuma tuni an sallame su.

Ya zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto, jami'an 'yan sanda sun ce ba su san wannan labarin ba.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari