Duba matakai 7 da aka dauka a Zamfara domin magance matsalar tsaro


Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ayyana daukar matakai bakwai da ta ce za su kawo sauki game da hare-haren da 'yan bindiga suke kai wa al'ummar jihar.

Eata sanarwa da Kwamishinan rundunar, Ayuba N. Elkanah ya aike wa manema labarai ranar Lahadi ta jaddada matakin da gwamnan jihar Mohammed Bello Matawalle ya bayar da umarnin dauka domin shawo kan matsalar.

Mun zayyano matakan kamar yada Kwamishina ya bayyana:

An rufe dukkan kasuwannin da ke ci mako-mako a fadin jihar sai abin da hali ya yi.

An ha hana sayar da fetr a jarkoki

An hana zirga-zirgar babura da babur mai kafa uku wato Keke Napep a Gusau babban birnin jihar daga karfe takwas na dare zuwa karfe shida na safe, yayin da aka hana yin hakan a kananan hukumomin da ke wajen Gusau daga shida na dare zuwa shida na safe.

An hana dukkan gidajen mai sayar da fetur da ya wuce na naira dubu goma ga motocin haya.

An haramta daukar itace a dukkan fadin jihar.

An dakatar da daukar dabbobi a fitar da su daga jihar, sanna dole a gudanar da cikakken bincike kan dukkan dabbobin da za a shiga da su jihar.

An hana 'yan acaba daukar mutum fiye da biyu a lokaci daya

Mahukunta sun yi amanar cewa gungun 'yan bindigar suna amfani da wadannan ayyukan tattalin arziki don kai hare -haren ga al'ummomi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara, Ayuba Elkanah, ya shaida wa manema labarai a Gusau babban birnin kasar, cewa an umarci hukumomin tsaro da su aiwatar da sabbin matakan da gwamnati ta sanar.

Najeriya na fama da matsalar kashe-kashen mutane da ta yi muni da kuma yan bindigar da ke sace mutane don karbar kudin fansa .

Ga dukan alamu hukumomi da iyalai da kuma al'umomi suna ɗaukar matakai don shawo kan matsalar.

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN