Duba jerin sunayen shugabannin Taliban da yadda tsarin shugabancinsu yake


Bayan da Shugaba Ashraf Ghani ya tsere ƙasashen waje kuma gwamnatinsa ta rushe, yanzu ƙungiyar Taliban ce take iko da Afghanistan.

A halin da ake ciki ba a san wanda zai jagoranci miƙa mulkin da masu iƙirarin jihadin suka ce zai kasance cikin "lumana" kuma ba tare da "ramuwar gayya ba".

Amma wane ne ke jagorantar Taliban a yanzu?

1. Hibatullah Akhundzada

Hibatullah Akhundzada ya zama shugaban Taliban ranar 25 ga Mayu a 2016, bayan mutuwar Akhtar Mansour, wanda aka kashe a wani harin Amurka bayan jagorantar ƙungiyar tsawon kusan shekara guda.

A shekarun 1980, ya fafata a yaƙin da aka yi a Afghanistan tsakaninta da ƴan Soviet, amma ya fi yin suna a matsayin shugaban addini fiye da kwamandan soji.

Akhundaza ya yi aiki a matsayin shugaban kotunan Shari'a a shekarun 1990.

Bayan da ta ƙwace mulki a karon farko a shekarun 1990, ƙungiyar Taliban ta ƙaddamar tare da goyon bayan hukunce-hukunce a tsarin addinin Musulunci: suna kashe mutanen da aka kama da laifin kisa a bainar jama'a da mazinata sannan suna yanke hannuwan ɓarayi.

Ƙarƙashin jagoranci Mullah Mohammed Omar (wanda ake tunanin ya rasu a shekarar 2013), Taliban ta haramta kallon talabijin da sauraren kiɗa da kallon fina-finai da kwalliya kuma sun hana yara mata ƴan sama da shekara 10 zuwa makaranta.

Mullah Mohammed Omar

ASALIN HOTON,EPA

Bayanan hoto,

Tsohon shugaban Taliban Mullah Mohammed Omar, wanda ya rasu a shekarar 2013

Ana tunanin Akhundzada na da shekaru tsakanin 60 zuwa 70 kuma ya yi mafi yawan rayuwarsa a Afghanistan.

Sai dai, a cewar ƙwararru yana da alaƙa mai ƙarfi da Quetta Shura, shugabannin Taliban na Afghanistan da ake tunanin suna zaune a birnin Quetta na Pakistan.

A matsayinsa na babban kwamandan ƙungiyar, Akhundzada na ke jagorantar ɓangarorin siyasa da soji da addini.

Taliban Structure

2. Abdul Ghani Baradar

Mullah Abdul Ghani Baradar na ɗaya daga cikin mutane huɗu da suka kafa Taliban a Afghanistan a 1994.

Ya zama babban jigo bayan da aka hamɓarar da Taliban a yaƙin da Amurka ta jagoranta a 2001.

Amma an kama shi a wani samame da dakarun Amurka da Pakistan suka kai a birnin Karachi da ke kudancin Pakistan a cikin watan Fabrairun 2010.

Taliban delegation headed by Abdul Ghani Baradar (C), the groups deputy leader, are seen leaving the hotel after attending the meeting on Afghan peace with the participation of delegations from Russia, China, the US, Pakistan in March 2021

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,

Mullah Abdul Ghani Baradar na ɗaya daga cikin mutane huɗu da suka kafa Taliban a Afghanistan

Ya kasance a gidan yari tsawon wata takwas kafin a sake shi ƙarƙashin wani tsari na son kawo zaman lafiya kuma ya zama shugaban siyasarsu a Qatar tun watan Janairun 2019.

A 2020, ya zama shugaban Taliban na farko da ya yi magana ga-da-ga da shugaban Amurka bayan da ya tattauna da Donald Trump.

Yanzu, Abdul Ghani Baradar shi ne babban jagoran siyasa na ƙungiyar Taliban.

"Mun yi nasara yadda ba mu yi tunani ba... Yanzu abun da ya rage shi ne yadda za mu yi wa mutane aiki kuma mu tsare su," kamar yadda aka Baradar ya ce a wata sanarwa da aka naɗa a Doha, babban birnin Qatar inda ya kasance cikin tawagar Taliban da ke tattaunawar zama lafiya.

Mike Pompeo and Abdul Ghani Baradar

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,

Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da Abdul Ghani Baradar lokacin da suka gana a Satumban 2020 a Doha

3. Mohammad Yaqoob

Mohamed Yaqoob shi ne ɗan Mullah Mohammed Omar wanda ya assasa ƙungiyar Taliban.

Ana tunanin shekarunsa sun haura 30 da kaɗan kuma a halin yanzu shi ne ke jagorantar ayyukan soji na ƙungiyar.

Bayan rasuwar tsohon shugaban Taliban Akhtar Mansour a 2016, wasu mayaƙan sun so a naɗa Yaqoob a matsayin babban kwamandan ƙungiyar, amma wasu suka ki amincewa suna ganin ya yi yarinta kuma ba shi da ƙwarewa.

A cewar kafofin yaɗa labarai na ƙasar. Yaqoob na zaune a Afghanistan.

4. Sirajuddin Haqqani

Haqqani shi ma ɗaya ne daga cikin manyan kungiyar.

Bayan mutuwar mahaifinsa, Jalaluddin Haqqani, ya zama sabon shugaban ɓangaren Haqqani, wanda aka ɗora wa alhakin mafi yawa daga cikin munanan hare-haren da aka kai a Afghanistan kan dakarun ƙasar da ƙawayensu na Yamma a shekarun baya-bayan nan.

Ɓangaren Haqqani a yanzu na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ƴan bindiga masu ƙarfin iko kuma waɗanda ake jin tsoron su a yankin. Wasu na cewa ma ta fi Ƙungiyar IS ƙarfi a Afghanistan.

FBI poster on the Haqqni network

ASALIN HOTON,FBI

Bayanan hoto,

Bangaren Haqqani a yanzu na daga cikin kungiyoyin masu ta da kayar baya masu matukar karfi da kuma ake jin tsoron su

Ƙungiyar, wadda Amurka ta ayyana a matsayin ta ta'addanci, na sa ido kan ɓangaren kuɗi da sojoji a iyakar Pakistan da Afghanistan.

Ana tunanin shekarun Haqqani ba su wuce 45 ba kuma ba a san a inda ya ke a zaune ba.

5. Abdul Hakeem

A Satumban 2020, Taliban ta naɗa Hakeem sabon shugaban tawagarta da ke tattaunawa a Doha.

Ana tunanin shekarunsa kusan 60 kuma yana da makarantar Islamiya a Quetta, Pakistan inda kuma yake sa ido kan ɓangaren shari'a na Taliban.

Shugabannin Taliban da dama sun nemi mafaka a Quetta inda daga nan ne suke jagorantar kungiyar.

Sai dai Pakistan ta musanta batun 'Querra Shura'.

Haka kuma, Hakeem ne ke jagorantar majalisar malaman addini mai karfin fada a ji kuma ana tunanin yana daya daga cikin manyan makusantan babban kwamanda Akhundzada.

Rahotun BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN