-->

Ads

Duba hotunan jariri da mahaifiyarsa ta ce Annabi ne ya dawo a jihar Kebbi

Duba hotunan jariri da mahaifiyarsa ta ce Annabi ne ya dawo a jihar Kebbi


Da karfe 12:48 na ranar Alhamis 26 ga watan Agusta, yansandan jihar Kebbi sun gurfanar da wata matar aure main suna Binta Isah a gaban Kotun shari'ar Musulunci na 1 da ke unguwar Nassarawa a garin Birnin kebbi tare da mijinta mai suna Aliyu Isah, bayan matar tare da mijinta sun yi ikirarin cewa dansu Muhammad Basiru "Annabi" ne. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Latsa nan ka karanta cikakken labarin  https://www.isyaku.com/2021/08/kotu-birnin-kebbi-ta-tura-uwa-da-uba.htmlBayan Alkali Mu'awiyya Umar Birnin kebbi ya saurare su tare da tambayasu ko abin da ake tuhumarsu sun aikata? sun sake ikirari a gaban Kotu cewa tabbas dansu "Annabi" ne tare da bayar da dalillai da ya sa suka ce haka.

Wadannan dalilai sun danganci dalilai na zargin yi wa Binta wahayi daga Annabi Manzon tsira, kamar yadda ta ce. Binta ta gaya wa Kotu cewa " Ina magana da Annabi, har da Nana Fatima".


Yana da kyau a duba lafiyar kwakwalwar Aliyu da Binta 

Masana sun yi tsokaci cewa yana da kyau a duba lafiyar wadannan ma'aurata domin a tabbatar cewa suna da cikakken lafiyar hankali da kwakwalwa. Duba da yadda lamarin ke tafiya ta hanyar jajircewa da wadannan ma'aurata suka yi kan ikirarin da suka yi cewa dansu mai wata tara da haihuwa Basiru "Annabi" duk da rikici da kwaramniya da yin hakan ya jawo masu, amma suka dage kan ikirarinsu har a cikin Kotu a gaban Alkali.

https://www.facebook.com/isyakulabari/videos/1103834420148378/

0 Response to "Duba hotunan jariri da mahaifiyarsa ta ce Annabi ne ya dawo a jihar Kebbi"

Post a Comment

Rubuta ra ayin ka

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN