Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadin malalewar unguwanni a karsar United Kingdom UK, lamari da ya sa magudanan ruwa suka cika har suka batse. Sakamakon haka mutane ke ta kokarin ganin sun taimaka wa kansu bisa wannan dalili. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.
Ana cikin haka ne, wani mazauni Glasgow, wanda har yanzu ya kasa ficewa daga gidansa sakamakon ambaliyar ruwan, ya gano wani abin mamaki..
Gavin Millar, ya dauki hotunan wata mata mai siffan Ayu tana iyo a cikin ruwan. Ya dauki hoton ne daga kan benen gidasa da ke Battlefield Gardens, wanda ke sashen kudancin birnin Gasgow ranar 7 ga watan Agusta.
Sai dai daga bisani an gano cewa wata mace ce ta saka rabin tufan Zabaya tana iyo domin a dauketa hoto.